INEC Ta Yi Fatali da Sanya Sojoji a Tsarin Zaben Najeriya, An Ji Dalili
- Hukumar INEC da ke shirya wa da kula da zabuka a Najeriya ta yi magana game mayar da tura jami'an rundunar sojin Najeriya filayen zabe
- Shugaban hukumar, Joash Amupitan ya bayyana illar yin hakan yayin da a gefe guda ya bayyana wanda doka ta dora wa alhakin kare kayan zabe
- Yayin da zaben 2027 ke gabatowa, Farfesa Joash Amupitan ya fadi gabar da za a iya amfani da sojoji dangane da abubuwan da suka shafi zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce bai kamata a riƙa tura rundunar sojoji domin tsaron zaɓe a matsayin al'ada ba,.
Ya bayyana cewa za a iya amincewa da aika dakaru ne sai dai idan yanayin tsaro ya tilasta hakan domin tallafa wa hukumomin farar hula.

Source: Facebook
Daily Trust ta kawo labarin cewa Amupitan, wanda Daraktan Shari'a na INEC, Alhassan Umar, ya wakilta, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis 30 ga watan Yuli, 2026 yayin da yake gabatar da muhimmin jawabi a wani taron karawa juna sani da aka gudanar a Abuja.
Matsayar INEC kan aiki da sojoji
A ruwayar jaridar Punch, Amupitan ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya fayyace rawar da kowace hukuma ke takawa wajen gudanar da zaɓe.
Shugaban hukumar zaben ya kara da cewa INEC ce ke da alhakin shirya da gudanar da zaɓe, yayin da Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ke jagorantar ayyukan tsaron zaɓe.
A cewarsa:
"Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya ya fayyace ayyukan hukumomin da ke da hannu a tsarin zaɓe. INEC ce ke da alhakin shirya, gudanarwa da sa ido kan zaɓe, yayin da Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ke jagorantar tsaron zaɓe ƙarƙashin Kwamitin Haɗin Gwiwar Hukumomi kan Tsaron Zaɓe."
INEC za ta iya aiki da sojoji
Ya bayyana cewa rawar da sojoji ke takawa ita ce ta bayar da goyon baya, ba ta jagoranci ayyukan zaɓe ba, tare da kare tsaro ba tare da tsoma baki cikin siyasa ba.
Amupitan ya ce ayyukan da sojoji za su iya yi idan an buƙaci hakan sun haɗa da kare muhimman kadarorin ƙasa da tsaron manyan gine-ginen gwamnati.
Sannan za su iya taimakawa wajen jigilar kayayyakin zaɓe masu muhimmanci idan ya zama dole, da kuma tallafa wa hukumomin farar hula a lokutan da ake buƙatar ƙarin matakan tsaro.
Ya ce wannan tsari ba ya rage muhimmancin rundunar sojoji, sai dai yana tabbatar da cewa gudanar da zaɓe ya ci gaba da kasancewa karkashin ikon farar hula, tare da ba da damar samun taimakon tsaro idan wani yanayi na musamman ya taso.
INEC ta kwantar da hankulan jama'a
A wani labarin, kun ji cewa yayin da ake shirin gudanar da zaben 2027, Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya yi alkawari ga 'yan Najeriya tare da kwantar masu da hankali game da sahihancin sakamako.
Joash Amupitan ya yaba wa Janar Abdulsalami Abubakar saboda gudunmawarsa wajen tabbatar da dimokuraɗiyya da zaman lafiya yayin da kasar ke kusanto wani gagarumin lokaci na zabe mai cike da adawa.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da ranakun zaɓen 2027, tana roƙon 'yan Najeriya su ba hukumar cikakken goyon baya domin gudanar da sahihin zaɓe da kowa zai aminta da shi.
Asali: Legit.ng


