Trump Ya Fadi Zabin Amurka tsakanin Sulhu da Yaki a Iran

Trump Ya Fadi Zabin Amurka tsakanin Sulhu da Yaki a Iran

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka na ci gaba da tattaunawa da Iran domin kauce wa sabon rikici duk da akwai shirin yaki a kasa
  • Trump, wanda da farko ya shigar wa Isra'ila yakin ne ya yi ikirarin cewa Amurka ta shirya kai babban hari kafin Iran ta nemi a yi sulhu
  • Ya jaddada cewa ba zai yarda Iran ta mallaki makamin nukiliya ba tare da bayyana zabinsa tsakanin ci gaba da yaki da tabbatar da an samu yarjejeniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

USA – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa zai fi son cimma yarjejeniya da Iran maimakon daukar matakin soja, yana mai cewa ba ya son a kashe mutane.

Da yake jawabi a birnin Las Vegas na jihar Nevada, Trump ya ce Washington na ci gaba da tattaunawa da Tehran, kuma yana fatan bangarorin za su cimma matsaya ba tare da sake barkewar rikici ba.

Kara karanta wannan

Rahoto daga Isra'ila ya tona asirin yadda Trump ya shiga tsaka mai wuya kan Iran

Amurka ta fadi zabinta a yaki da Iran
Shugaban kasar Amurka Donald Trump Hoto: Getty
Source: Getty Images

Kafar Aljazeera ta wallafa cewa Trump ya yi ikirarin cewa Amurka ta kusa kaddamar da abin da ya kira hari mafi girma tun bayan yakin duniya na biyu.

Iran ta nemi sulhu - Trump

A jawabin Trump, ya bayyana cewa bayan shirin yakin, sai jami'an Iran suka tuntube shi suna rokon kada a kai harin, tare da neman a koma teburin tattaunawa.

A cewarsa:

"Mun riga mun shirya kai hari mafi girma tun bayan yakin duniya na biyu, sai suka kira ni suka ce, 'Don Allah kada ku yi hakan. Mu zauna mu tattauna.'"
Amurka ta ce ana samun haske a ganawa da Iran
Shugaban kasar Iran Masoud Pazeshkian Hoto: Masoud Pazeshkian
Source: Facebook

Trump ya kara da cewa:

"Na fi son cimma yarjejeniya da Iran saboda ba na son kashe mutane."

Matsayar Amurka kan nukiliya a Iran

Shugaban kasar Amurka, Donald J Trump ya sake jaddada matsayinsa cewa ba za a bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.

Ya ce tattaunawar da ake yi yanzu kamar za ta haifar da mai ido, amma Amurka ba za ta amince da wasu daga cikin bukatun da ta ja wa layi ba.

Kara karanta wannan

"Ni masoyinsa ne": Davido ya faɗi yadda ya ke musayar sakonni da Ronaldo

Shugaban Amurka da abokan huldar kasarsa sun dade suna adawa da duk wani yunkurin Iran na mallakar makamshin nukiya.

Sai dai Iran ta sha nanata cewa babu maganar samar da makamin nukiliya a cikin tsare-tsarenta, amma Amurka da kasashe irin Isra'ila sun ki amincewa da hakan.

Trump ya yi maganar yarjejeniya da Iran

A baya, mun kawo labarin cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ana iya cimma yarjejeniya da Iran kan sake buɗe mashigar Hormuz tun ranar Laraba, amma ya yi gargadin kan batun.

Harkar zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar, wadda hanya ce mai muhimmanci wajen jigilar mai da iskar gas a duniya, ta zama babban abin takaddama a tattaunawar da ake ta samun matsala a baya.

Donald Trump ya yi gargadin cewa akwai shirin mummunan hari da kasarsa ta tanada mutukar aka gaza cimma matsayar da ya kwantawa Amurka da 'yan abokan huldar kasar,

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng