Hankula Sun Tashi da 'Yan Bindiga Suka Nemi N80m bayan Sace Basarake

Hankula Sun Tashi da 'Yan Bindiga Suka Nemi N80m bayan Sace Basarake

  • Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun sace dagacin Patiko da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja
  • Mazauna yankin sun ce maharan sun nemi a biya Naira miliyan 80 a matsayin kudin fansa domin a sako shi
  • An ce hare-haren da 'yan bindiga suke kaiwa yankin sun tilasta wa manoma barin gonakinsu na noma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Minna, jihar Neja - Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun sace dagacin ƙauyen Patiko, Mallam Haruna Abubakar, a gundumar Zugurma da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja.

Wani mazaunin yankin mai suna Aliyu Usman ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun mamaye ƙauyen ne da tsakar daren ranar Juma’a, 31 ga watan Yulin 2026.

'Yan bindiga sun sace basarake a Neja
Taswirar jihar Neja, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Aliyu Usman ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa maharan sun riƙa harbe-harbe ba gaira ba dalili tare da kewaye gidan hakimin kafin su tafi da shi.

Kara karanta wannan

Badakalar PFIPC: Adeniyi ya yi sabuwar fallasa yayin da yake tsare a hannun 'yan sanda

An nemi N80m kudin fansa

A cewar Aliyu Usman, ‘yan bindigar sun kira wasu mutane ranar Asabar, 1 ga watan Agustan 2026 inda suka nemi a biya Naira miliyan 80 kafin a sako dagacin.

Aliyu Usman ya ƙara da cewa maharan sun kuma kai hari a ƙauyen Fanga da ke karamar hukumar Mashegu. An ce ‘yan bindigar sun kashe wani manomi tare da sace wasu mutum huɗu a yayin harin.

Hare-hare sun addabi Mashegu

Aliyu Usman ya ce karamar hukumar Mashegu ta fuskanci hare-hare masu yawa a cikin makon da ya gabata. Ya ce an sace mutane da dama, an kwashe shanu masu yawa, yayin da wasu mazauna yankin suka tsere daga gidajensu.

“Muna rayuwa cikin fargaba a kowane lokaci saboda ‘yan bindiga na iya zuwa su kai mana hari a duk lokacin da suka ga dama.” Inji shi

Manoma sun bar gonakinsu

Aliyu Usman ya ce tabarbarewar tsaro a yankin ta hana manoma gudanar da ayyukan noma a wannan daminar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali da 'yan bindiga suka kashe sojoji da sace mutane a Zamfara

Ya ce noma ne babban hanyar da al’ummar yankin ke samun abinci, amma yanzu sun bar gonakinsu saboda tsoron hare-haren ‘yan bindiga.

Ya ƙara da cewa:

“Rayuwarmu ta lalace saboda mun bar gonakinmu. Muna buƙatar gwamnati ta gaggauta shiga cikin lamarin.”

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya ce zai bincika lamarin sannan ya bayar da cikakken karin bayani.

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, bai sake bayar da wani bayani ba dangane da harin da 'yan bindigan suka kai.

'Yan bindga sun yi barna a Neja
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

'Yan bindiga sun kona mutane a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun hallaka akalla mutum 12 ciki har da shida da aka ƙona da ransu, bayan harin da suka kai a jihar Sokoto.

'Yan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Lajinge da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Majiyoyi sun bayyana cewa mutum shida sun ƙone da ransu bayan ƴan bindigar sun kewaye wani ɗaki da suka shiga suka fake.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng