Ta Faru Ta Kare: Sanata Hanga Ya Bar Tafiyar Kwankwaso, Ya Fice daga Jam'iyyar NDC

Ta Faru Ta Kare: Sanata Hanga Ya Bar Tafiyar Kwankwaso, Ya Fice daga Jam'iyyar NDC

  • Sanata Rufai Hanga ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), yana mai cewa ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari
  • Sanatan Kano ta Tsakiya ya ce zai mayar da hankali kan wasu harkoki da manufofinsa na kashin kai bayan barin jam'iyyar
  • Hanga ya gode wa shugabanni da mambobin NDC bisa goyon baya da haɗin kan da suka ba shi a lokacin da yake cikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Kano - Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Rufai Hanga, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NDC.

Sanatan, wanda kuma shi ne mataimakin bulalar marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 3 ga Agustan 2026 da ya aikewa shugaban jam'iyyar NDC na mazabarsa.

Kara karanta wannan

INEC ta fitar da sunan dan takarar PDP da zai kara da Bola Tinubu a 2027

Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Hanga ya fice daga jam'iyyar NDC.
Sanata Rufai Hanga da ya yi murabus daga jam'iyyar NDC. Hoto: Rufai Hanga
Source: Facebook

Dalilin ficewar Sanata Hanga daga NDC

A cikin wasiƙar, Hanga ya ce ya yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar ne bayan dogon nazari da tunani, in ji rahoton Daily Nigerian Hausa.

Ya bayyana cewa ya bar jam'iyyar ne domin ya mayar da hankali kan wasu harkokinsa da kuma manufofinsa na kashin kai.

Sanatan bai bayyana wasu ƙarin bayanai kan irin waɗannan manufofi ko matakin siyasa da zai ɗauka nan gaba ba.

Ya gode wa shugabanni da mambobin NDC

Hanga ya nuna godiyarsa ga shugabannin jam'iyyar a matakin mazaɓa da sauran mambobi bisa damar da suka ba shi da kuma haɗin kan da suka nuna masa a lokacin da yake cikin jam'iyyar.

Ya ce zai ci gaba da tuna kyakkyawar alaƙar da ya gina da mambobin jam'iyyar da kuma abubuwan da suka gudanar tare a harkokin siyasa.

Ya nemi a cire sunansa daga rajistar NDC

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa, sanatan ya ce ya haɗa katin shaidar zama mambansa na jam'iyyar tare da wasiƙar murabus ɗin.

Kara karanta wannan

APC: Kwankwaso ya kwashe mutanen Abba Kabir da Ganduje zuwa NDC

Ya kuma buƙaci shugabannin jam'iyyar su cire sunansa daga rajistar mambobin NDC a matakin mazaɓarsa.

A ƙarshe, Sanata Rufai Hanga ya yi wa jam'iyyar da dukkan mambobinta fatan alheri a dukkan harkokinsu na gaba.

Sanata Hanga ya dade yana shiri

Sanata Hanga ya fice daga NDC kwanaki bayan ya gana da Tinubu
Sanata Barau Jibrin ya jagoranci su Sanata Rufai Hanga sun gana da Shugaba Bola Tinubu a Abuja. Hoto: @barauijibrin
Source: Facebook

Ko a makon da ya gabata, an samu rahoto cewa Rufai Sani Hanga, ya fara tuntubar manyan masu ruwa da tsaki a mazabarsa gabanin yiwuwar sauya sheka daga jam'iyyar NDC zuwa APC.

Sanata Hanga ya gana da masu tsara harkokinsa daga kananan hukumomi 15 na Kano ta Tsakiya domin tattauna batun sauya sheka.

The Sun ta kawo labarin cewa rahotanni sun ce ya kuma gudanar da ganawar sirri da Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Barau ya kai Hanga wajen Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Rufai Hanga mai wakiltar Kano ta Tsakiya ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Kosan Waka: An fitar da lokacin jana'izar fitaccen mawakin Gwamnan Kano

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya jagoranci Hanga da tsohon Sanata Kabiru Gaya zuwa ganawar da suka yi da Tinubu.

Ganawar ta zo ne yayin da ake ta raɗe-raɗin cewa Sanata Rufai Hanga na shirin ficewa daga jam'iyyar NDC zuwa APC bayan tuntuba da ya ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com