Tashin Hankali da 'Yan Bindiga Suka Kashe Sojoji da Sace Mutane a Zamfara
- Rahotanni sun ce ƴan bindiga sun kashe aƙalla sojoji shida tare da yin garkuwa da fiye da mutum 70 a Kasuwar Daji
- An ce maharan sun mamaye sansanin sojoji kafin su shiga garin da harbe-harbe, inda suka kashe mutane
- Wani tsohon mataimakin kakakin majalisa ya ce an kwashe kayan abinci da sauran dukiyoyi daga shaguna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Jihar Zamfara - Rahotanni sun nuna cewa wasu ƴan bindiga da ake zargi sun kashe aƙalla sojoji shida tare da yin garkuwa da fiye da mutum 70 a jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun kai harin ne a garin Kasuwar Daji da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara.

Source: Twitter
Majiyoyi daga yankin sun shaida wa Vanguard ta wayar tarho cewa ƴan bindigar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren Asabar, 1 ga watan Agustan 2026 bayan sun mamaye sansanin sojojin da ke Kasuwar Daji.
Sun ce maharan sun kashe sojoji shida tare da yin garkuwa da fiye da mutum 70, kafin su shiga wasu shaguna suka kwashe dukiyoyi.
Yadda ƴan bindiga suka kai hari
Wani mazaunin garin da ya bayyana sunansa a matsayin Alhaji Aminu Kasuwar Daji ya ce ƴan bindigar sun shigo garin da yawa.
A cewarsa, da zarar sun isa, sai suka fara harbe-harbe ba tare da tsari ba domin mamaye sansanin sojojin da aka kafa domin kare yankin.
Aminu Kasuwar Daji ya roƙi gwamnatin jihar Zamfara da gwamnatin tarayya su kawo wa mutanen jihar ɗauki saboda matsalar rashin tsaro.
“Kiranmu ga gwamnatin jihar Zamfara da gwamnatin tarayya shi ne su kawo wa mutanen Zamfara ɗauki kan matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar. Muna cikin haɗari matuƙa, domin idan ƴan bindiga za su iya mamaye sojoji su yi nasara wajen kai hari kan fararen hula, to lallai muna cikin mawuyacin hali.” In ji shi

Kara karanta wannan
"Shiri ne": Yadda aka kashe babban soja mahaddacin Kur'ani mai shirin kafa tarihi
Tsohon mataimakin kakakin majalisa ya yi magana
Tsohon mataimakin kakakin majalisar dokoki, Hon. Namadi Kasuwar Daji, ya tabbatar da cewa ƴan bindiga sun kai hari a garinsu tare da yin garkuwa da wasu mazauna yankin.
Ya ce bai kasance a garin ba a lokacin harin saboda ya yi tafiya zuwa wani waje a wajen jihar, amma danginsa sun kira shi suka sanar da shi abin da ya faru.
A cewarsa:
“An sanar da ni cewa ƴan bindigan sun kashe wasu sojoji, amma ba a gaya mini ainihin adadinsu ba. An kuma sanar da ni cewa bayan sun kwashe kayan abinci, abubuwan sha da sauran dukiyoyi daga shaguna, sun yi garkuwa da wasu mazauna yankin suka tafi da su cikin daji.”

Source: Original
Ƴan sanda sun ce ba su samu labari ba
Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce bai samu labarin harin da aka kai Kasuwar Daji ba.
Sai dai ya yi alƙawarin zai sake kira bayan ya tuntuɓi shugaban ƴan sanda da ke yankin.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, jami’in bai amsa kiraye-kirayen da aka yi masa domin jin ƙarin bayani kan alƙawarin da ya yi ba.
'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar 'yan sandan jihar Sokoto sun dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Sokoto.
Jami'an 'yan sandan sun kuma ceto tumaki 43 da 'yan bindiga suka sace daga kauyen Anada da ke karamar hukumar Binji.
Asali: Legit.ng

