Yan Arewa Sun Taso Kiristoci a Gaba kan Tinubu, Sun Sha Alwashi kan Zaben 2027
- Wata kungiya a Arewacin Najeriya ta soki NCEF kan bukatar Tinubu ya hakura da takarar 2027, yana cewa 'yan Najeriya ne ke yanke hukunci
- Ta gargadi shugabannin addini kada su mayar da mumbari wajen siyasa, yana bukatar masu goyon bayan dan takara su fito fili su bayyana matsayarsu
- Ya ce gwamnatin Tinubu na fuskantar tarin kalubalen da ta gada, tare da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki, noma, mai da shirye-shiryen jin kai ga al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wata kungiya a Arewacin Najeriya da ake kira Think Tank ta yi magana game da nasarar zaben Bola Tinubu a 2027.
Ƙungiyar ta bayyana kwarin gwiwa kan nasarar Tinubu yayin martani ga ikirarin cewa shugaban zai samu matsala.

Source: Facebook
Shugaban kungiyar, Muhammad Alhaji Yakubu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Tribune ta samu.
Zaben Tinubu: An caccaki ƙungiyar Kiristoci
Yakubu ya bayyana cewa matsayar kungiyar dattawan Kiristan yunkuri ne na hada addini da siyasa tare da matsa wa shugaban kasa lamba.
Ya soki Kungiyar Tsofaffin Dattawan Kirista ta Kasa (NCEF) kan kiranta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya hakura da neman wa'adi na biyu a 2027, ya ce babu wata kungiyar addini da ke da ikon yanke wa 'yan Najeriya wanda za su zaba.
Yakubu ya jaddada cewa kundin tsarin mulki ya bai wa 'yan Najeriya kadai ikon zabar wanda zai jagorance su, ya ce babu wata kungiyar addini ko ta matsin lamba da za ta iya hana Shugaba Tinubu tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027.

Source: Twitter
Zargin da ake yi wa kungiyar Kiristoci
A cewarsa, idan Allah Ya nufa kuma 'yan Najeriya suka sake zabarsa, babu wani matsin lamba da zai hana hakan.
Yakubu ya kuma zargi kungiyar da amfani da halin da kasa ke ciki domin cimma manufofin siyasa, ya bukaci malaman da ke goyon bayan wani dan takara su fito fili su bayyana matsayarsu maimakon boyewa a bayan matsalolin kasa.
Ya ce idan wadannan malaman addini na yakin neman zaben wani dan takara ne, su bayyana hakan a sarari, ya gargade su cewa yin siyasa a boye na iya sa su rasa mutunci da kima da jama'a ke yi musu.
Jagoran ƙungiyar ya kuma bukaci shugabannin addini su guji duk wani abu da zai kara rarrabuwar kawuna ta fuskar siyasa da addini.
A cewarsa, idan wani na son shiga siyasa kai tsaye, ya kamata ya ajiye rawanin limanci ya shiga harkar siyasa a fili, cewar Daily Post.
Yakubu ya bayyana cewa ya kamata a tantance gwamnatin Tinubu bisa manyan kalubalen da ta gada tsawon shekaru masu yawa.
Ya kara da cewa karuwar yawan jama'a ta zarce ci gaban ababen more rayuwa da albarkatun kasa, saboda haka, ba zai yiwu a samu ci gaba cikin gaggawa ba duk da kokarin da gwamnati ke yi.
Gagarumin aikin gwamnatin Tinubu a Kano
Mun ba ku labarin cewa hukumar FERMA ta fara gyaran titin Kano Eastern Bypass mai tsawon kilomita 13 domin rage cunkoson ababen hawa a cikin birnin Kano.
Ana gudanar da aikin ta hanyar amfani da ma’aikatan hukumar kai tsaye tare da tura kusan ma’aikata 70 zuwa titin.
Ana sa ran kammala aikin cikin makonni biyu bayan fara shi a ranar 23 ga Yulin shekarar 2026 da muke ciki.
Asali: Legit.ng

