'Yan Ta'adda Sun Kutsa Asibiti a Neja, Babban Likita Ya Fada Hannun Miyagu
- 'Yan ta'adda dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Najeriya na tarayyar Najeriya
- Tsagerun 'yan ta'addan sun kutsa cikin wani asibiti inda suka yi awon gaba da babban likita ba tare da sace kowa ba
- Mutanen yankin sun yi zargin cewa akwai abin da 'yan ta'addan suke kullawa shiyasa suka yi garkuwa da likitan zuwa cikin daji
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - ’Yan ta’adda da ke gudanar da ayyukansu a kewayen dajin Kainji sun kai hari a wani asibiti a jihar Neja.
'Yan ta'addan sun yi garkuwa da wani likita mai suna Anthony Enahoro, a gundumar Wawa da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja.

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta ce a cewar mazauna yankin, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na daren ranar Laraba, 22 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
Sojojin sama sun toshe kofofin tsira ga 'yan ta'adda yayin da aka hallaka tsageru masu yawa
'Yan ta'adda sun kai hari a Neja
Garin Wawa wuri ne da ke da dakarun sojoji, ciki har da gidan yari inda ake tsare da mambobin Boko Haram da sauran waɗanda ake zargin ‘yan ta’adda ne.
‘Yan ta’adda sun yi ƙoƙarin kutsa kai cikin garin mai tsaro a watan Oktoban 2022 amma sojoji suka samu nasarar dakile su.
Kwanan nan, wata takardar sirri da ta fito daga Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta bayyana cewa ‘yan ta’addan Boko Haram suna shirin kai hari gidan yarin domin ’yantar da abokan aikinsu.
'Yan ta'adda sun sace likita
Wani shugaban matasan yankin ya bayyana an sace Mista Enahoro, wanda shi ne mamallakin asibitin Hope, a asibitinsa da ke kan titin Wawa zuwa Lima.
Mazauna yankin sun ce duk da cewa akwai mutane da dama a wurin, likitan ne kawai aka tafi da shi, shafin @mobilsingniger ya kawo labarin
Mutanen yankin suna zargin cewa an sace likitan ne domin ya ba da magani ga mayakan da suka ji rauni ko kuma waɗanda ba su da lafiya.
“Shi likita ne kuma muna zargin cewa an yi garkuwa da shi ne domin ya duba ‘yan ta’addan, domin shi ne ɗaya daga cikin ƙwararrun likitocin da muke da su a ƙasar Borgu a halin yanzu."
- Shugaban matasa
Wadanne 'yan ta'adda ne suka kai harin?
Har yanzu ba a fito fili an tabbatar ko ƙungiyar Ansaru ce ke da hannu a sace Mista Enahoro ba, wadda ta samu ƙarfafa sakamakon kutsowar ƙungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) daga yankin Sahel zuwa yankin Kainji.
Sai dai, ana jin cewa wani tsagi na Boko Haram ƙarƙashin jagorancin Sadiku ne ke da babban tasiri a yankin da aka yi garkuwa da likitan.
Ƙungiyar ta gudanar da hare-hare da dama, ciki har da dasa bama-bamai a manyan hanyoyin da ke yankin.

Source: Original
Ba a ji ta bakin 'yan sanda ba
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba game da harin na daren Laraba.
Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, bai ba da amsar tambayar da aka yi masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
'Yan bindiga sun kashe sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun farmaki wani sansanin dakarun sojoji da ke kauyen Kemanji a jihar Kwara.
Harin wanda 'yan bindigan suka kai da misalin ƙarfe 3:00 na dare, ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji uku da kuma ƴan banga biyu.
Baya ga kisan da suka yi, maharan sun yi nasarar ƙwace motar yaƙi ta sojoji, makamai, harsashi masu yawa, da kuma babura 12 mallakin jami'an tsaro.
Asali: Legit.ng

