Jam'iyyar PDP
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya yi Allah wadai da hotun da ake yaɗawa ana cewa wai ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, ya faɗi masu hannu.
Sanata David Jimkuta da ke wakiltar Taraba ta Kudu ya ce har aikin acaba ya yi domin rufawa kansa asiri kafin shiga Majalisar Tarayya inda ya yabawa Nyesom Wike.
Jam'iyyar APC ta wanke kanta daga zargin cewa ta jefa rikici a PDP. APC ta yi wa Atiku zazzafan martani kan cewa tana amfani da Wike wajen hura wuta a PDP.
Dan Majalisar Wakilai daga jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji ya karɓi dubban magoya bayan PDP da sauran jam'iyyun adawa a jihar zuwa jam'iyyar APC.
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa idan aka bar ƴan Najeriya suka nuna fushinsu kan mulkin APC a 2027, ƴan adawa za su karbi mulki kamar yadda ta faru a Ghana.
Paul Ibe, mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya ce haɗa kan maoi gidansa Atiku Abubakar da Peter Obi zai kawo karshen mulkin APC.
Gwamnan Zamfara ya nada sabon kwamishina mai lura da muhalli yayin da da yi sauye sauye a gwamnati. Sabon kwamishinan ya maye gurbin wanda ya yi murabus.
Jigon jam'iyyar PDP mai adawa a Sokoto, Faruku Fada ya dauki nauyin yara har guda 1,000 domin yi musu kaciya kyauta a jihar saboda tallafawa iyayensu.
Babbbar jam'iyyar adawa reshen jihar Imo a Kudu maso Yamma ta kori ɗan majalisar wakilan tarayya, Imo Ugochinyere Ikeagwonu bisa zargin rashin ɗa'a.
Jam'iyyar PDP
Samu kari