2027: An Fara Zargin Obi Zai Yaudari 'Yan Arewa saboda Ya Muzguna Masu a baya

2027: An Fara Zargin Obi Zai Yaudari 'Yan Arewa saboda Ya Muzguna Masu a baya

  • Tsohon 'dan takarar shugaban kasa, Omoyole Sowore ya zargi Peter Obi da kokarin yi wa 'yan Arewa dadin baki yayin da zaben 2027 ke zuwa
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da tsohon 'dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya bayyana cewa Arewa ce kashin bayan tattalin arzikin Najeriya
  • Haka kuma ya shaida wa jama'a cewa yana da wasu manyan tsare-tsare da zai aiwatar idan ya samu damar zama shugaban kasa da za su farfado da shiyyar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC a zaben 2023, ya soki tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, inda ya zarge shi da riya dangane da sabbin kalamansa kan arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala ya sauya akalar siyasarsa bayan sanya labule da Peter Obi

Obi, wanda ke daga cikin manyan jam’iyyar hamayya ta ADC, ya bayyana cewa zai ba wa ci gaban Arewacin Najeriya fifiko, yana mai cewa yankin shi ne babbar kadara ta kasa.

Sowore ya soki kalaman Obi a kan Arewa
Tsofaffin yan takarar shugaban kasa, Omoloye Sowore da Peter Obi, Peter Obi Hoto: Omoloye Sowore/Mister Peter Obi
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a jawabin da ya yi a baya, Obi ya ce ya tsara yadda zai habaka bangaren noma saboda albakar da ke kasar Arewa.

Alkawarin Peter Obi ga 'yan Arewa

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Peter Obi ya yi alkawarin cewa babbar kadarar Najeriya ita ce Arewa, kuma yi duk abin da ya dace wajen dawo da martababar ba.

A cewar Obi:

“Babbar kadararmu tana Arewa. Manyan gonaki da ba a noma wa da ke Arewa su ne makomarmu. Za mu iya samun kudin shiga mai yawa daga noma fiye da man fetur, kuma dole ne mu fara yin hakan nan take.”
Sowore ya zargi Obi da korar yan Arewa daga Anambra
Omoyole Sowore, tsohon dan takarar shugaban Najeriya Hoto: Omoyole Sowore
Source: Facebook

Sai dai Sowore ya ce wannan magana ta Obi na da alaka da siyasa ne kawai, kuma yana kokarin jawo hankalin masu zabe daga Arewa.

Omoyole Sowore ya kara da cewa wannan matsayi na Obi ya saba da abubuwan da ya aikata lokacin da yake gwamnan Anambra.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Zaben shugaban kasar Najeriya zai yi zafi kamar yaki a 2027

An tona yadda Obi ya kori yan Arewa

Tsohon dan takarar shugaban kasa a AAC, Omoyole Sowore ya bayyana amincewa da ikirarin da Obi ya yi na cewa akwai tarin albarka a karkashin kasar Arewa.

Ya ce:

“Idan ka je Arewa, eh, za mu iya mayar da Arewa babbar kadara, amma kowanne bangare na Najeriya na iya zama kadara. Kowane inci na kasar nan kadara ce."
“Amma Obi yana kokarin faranta ran ‘yan Arewa ne yanzu. Shin ba wannan Obi din ba ne da ya saka ‘yan Arewa a cikin bas ya mayar da su shiyyarsu?”

Sowore ya kuma yi ikirarin cewa hulda daya tilo da Obi ya yi da ‘yan Arewa lokacin mulkinsa ita ce mayar da mabarata zuwa yankinsu.

“A wancan lokacin, ya manta cewa Arewa kadara ce ta Najeriya. Kada ku bari ya yaudare ku."

Ya bayyana cewa dukkannin yankunan Najeriya na da damar bunkasa tattalin arziki, don haka ya kamata a rika daukar su daidai ba tare da fifiko ga wani yanki ba.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda babban hadimin Tinubu ke zuga su Nafiu Bala su tarwatsa ADC

“Arewar Najeriya babbar kadara ce. Kudancin Najeriya ma babbar kadara ce. Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Yamma, da ko’ina ma kadara ce a kasar nan."

Obi, Kwankwaso za su iya aiki tare

A baya, mun wallafa cewa wani na kusa da Peter Obi ya bayyana cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya amince ya zama abokin takarar tsohon gwamnan Anambran a zaɓen 2027 mai zuwa.

Ibrahim Abdulkarim ya tabbatar da cewa an riga an tsara taron haɗin gwiwa tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya da kuma Obidients yayin da suka fara tallata iyayen gidansu ga yan Najeriya.

Kwankwaso ya taba cewa zai karɓi muƙamin mataimakin shugaban ƙasa na Peter Obi, muddin aka samar da amana, duk da ya girmi Obi a siyasance, lamarin da a yanzu magoya baya ke kokarin a tabbatar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng