Atiku Ya Yi wa Obasanjo Gori, Ya Tabo Batun Hana Tsohon Shugaban Wa'adi na 3

Atiku Ya Yi wa Obasanjo Gori, Ya Tabo Batun Hana Tsohon Shugaban Wa'adi na 3

  • Atiku da ke neman kujerar shugaban kasa a 2027 ya yi zazzafan martanu ga kalaman Olusegun Obasanjo da ya yi nadamar aiki da shi
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya taimaka wa Obasanjo lokacin da yake gidan yari da bayan ya samu ya shaki iskar yanci
  • Ya zargi Obasanjo da ƙoƙarin bayar da labarin abubuwan da suka faru ba dai-dai ba, yana mai cewa kundin tsarin mulki ya fi kowa muhimmanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya mayar da martani ga tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, kan kalaman da ya yi a kansa.

Atiku Abubakar da ke neman shugaban kasa ya bayyana cewa bai taɓa nadamar dakile yunƙurin wa'adi na uku ba, kuma tarihi ba zai canza ba saboda ra'ayin wani.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya kama sunan Atiku da ya ambaci babban kuskuren da ya yi a rayuwa

Atiku ya yi Obasanjo martani
Atiku Abubakar tare da Cif Obasanjo a wani taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa hakan na zuwa ne bayan Obasanjo ya bayyana zaɓen Atiku a matsayin mataimakinsa a zaɓen shugaban ƙasa na 1999 shi ne babban kuskuren da ya yi a lokacin mulkinsa.

Atiku ya dura kan Obasanjo

Daily Post ta kawo labarin cewa sai dai a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan hulɗa da jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Asabar, 1 ga watan Yuli, 2026 Atiku ya ce kalaman Obasanjo wani yunƙuri ne na sake rubuta tarihi.

Atiku ya ce matsayarsa ta adawa da yunƙurin wa'adi na uku ba ta taɓa sauyawa ba, yana mai cewa ya fifita kare dimokuraɗiyya da kundin tsarin mulkin Najeriya a kan biyayya ga mutum.

Atiku ya ce ya zabi ya dabbaka dimokuradiyya
Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar ADC a zaben shugaban kasa na 2027 Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Ya ce:

"Ina alfahari da cewa na yi adawa da batun wa'adi na uku. Ina alfahari da cewa na tsaya tsayin daka wajen kare Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya. Ba ni da wata nadama ko kaɗan kan dakile duk wani yunƙuri na lalata dimokuraɗiyyarmu saboda burin wani."

Kara karanta wannan

Netanyahu ya fadi matakin da sojojin Isra'ila za su dauka idan aka cafke shi

Atiku ya kare adawa da wa'adi na 3

A cewarsa, yaƙin da aka yi da batun wa'adi na uku ba yaƙi ne tsakanin mutane biyu ba, illa kare dimokuraɗiyyar Najeriya domin al'ummomi masu zuwa.

Atiku ya kuma yi ikirarin cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen dawowar Obasanjo siyasa bayan an sake shi daga gidan yari a wancan lokaci.

A kalamansa:

"Idan haushin Cif Obasanjo ya samo asali ne saboda na ƙi goyon bayan wa'adi na uku wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulki, to ina ɗaukar wannan a matsayin abin alfahari. Babu wani mutum da ya fi Tarayyar Najeriya girma. Kundin tsarin mulki shi ne mafi girma, kuma na zaɓi Najeriya a kan biyayya ga mutum."
"Tarihi ya nuna cewa lokacin da Cif Obasanjo yake gidan yari, na tsaya tare da shi. Na taimaka wa iyalansa, na yi aiki tare da sauran masu kishin ƙasa domin a sake shi, kuma ban taɓa daina gaskata cewa ya cancanci 'yanci ba."

Kara karanta wannan

'Ba yan adawa ba': Atiku ya fadi babban ƙalubalen Tinubu a zaɓen 2027

Ya ci gaba da cewa bayan Obasanjo ya samu 'yanci, ya karɓe shi, ya kula da shi, sannan ya yi amfani da dangantakarsa ta siyasa wajen taimaka masa har ya zama shugaban ƙasa.

Obasanjo ya yi nadamar aiki da Atiku

A baya, mun kawo labarin cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce zaben Atiku Abubakar a matsayin mataimakinsa a 1999 shi ne babban kuskuren da ya taba yi a rayuwarsa.

Cif Olusegun Obasanjo ya ce da zai sake samun dama, ba zai zabi Atiku a matsayin mataimakin shugaban kasa ba, tare da bayyana yadda ya tafiyar da gwamnati duk da sabin da ke tsakaninsu.

Tsohon shugaban kasar ya ce duk da sabanin da suka samu, bai bari hakan ya hana shi gudanar da mulkin Najeriya wajen samar da ayyukan da suka dace domin ci gaban kasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng