"Ba Zan Ci Amana ba," Abin da Gwamna Radda Ya Fada Wa Yusuf Buhari a Katsina

"Ba Zan Ci Amana ba," Abin da Gwamna Radda Ya Fada Wa Yusuf Buhari a Katsina

  • Gwamna Dikko Radda ya ja hankalin 'dan marigayi tsohon shugaban kasa, Yusuf Buhari kan takarar dan Majalisar tarayya da ya fito a APC
  • Malam Dikko Radda ya bayyana cewa ya ci gajiyar marigayi Buhari, don haka ba zai taba cin amanar iyalinsa bayan Allah ya masa rasuwa ba
  • Yusuf Buhari da yar uwarsa, Zahra Buhari sun kuma ziyarci Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman domin sa albarka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda ya tuna alherin da ya samu a zamansa da marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Malam Dikko ya ce ba zai taba manta abubuwan alheri da gajiyar da ya ci a zamansa da Buhari ba, don haka ba zai yi gigin cin amanar iyalan marigayin ba.

Kara karanta wannan

Dalilan da suka sanya Abba zabar Garo a mataimakin gwamnan Kano

Gwamna Dikko Radda.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda yana magana da tawagar Yusuf Buhari a fadar gwamnatinsa Hoto: Office of the Chief Press Secretary, Katsina state
Source: Facebook

Yusuf Buhari ya ziyarci Gwamnan Katsina

Jarridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Radda ya yi wannan bayanin ne ga tawagar Yusuf Buhari, dan marigayi Buhari lokacin da suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin Katsina.

Tawagar dai ta kunshi Yusuf Buhari da yar uwarsa, Zahra Buhari, da kuma masu ruwa da tsakin APC na kananan hukumomin Daura, Mai’adua da Sandamu.

Masu ruwa da tsakin sun ziyarci Dikko Radda ne don gabatar da Yusuf Buhari a matsayin ɗan takararsu na Majalisar Tarayya karkashin inuwar APC a zaben 2027 da ke tafe.

Da yake jawabi ga iyalin Buhari da ke cikin tawagar, Gwamna Radda ya bayyana cewa tun daga shekarar 2015 ya fara cin gajiyar marigayin, wanda hakan ya sa ba zai juya masu baya ba.

"Ba zan taɓa cin amanar iyalan Buhari ba. Na kasance wanda ya amfana da kyakkyawan sunansa tun zamanin CPC har zuwa yau.

Kara karanta wannan

Takarar 2027: Manyan 'yan siyasa sun raka Yusuf Buhari wajen gwamna Radda

"Buhari ya rasu yanzu, Allah Ya ji kan sa. Saboda haka, ina yi wa Yusuf fatan alheri a harkokin siyasa da ya shiga," in ji shi.

Gwamna Radda ya bude kofa ga kowa

Dangane da batun takarar da Yusuf Buhari zai nema, Gwamna Radda ya jaddada cewa a bisa tsarin dimokuraɗiyya, jam’iyyar APC ta na bai wa kowa 'yancin fitowa takara.

Ya ce hatta marigayi Buhari ya taba fafatawa da wasu a zabuka kafin ya kai ga nasara, don haka Yusuf Buhari yana da damar gwada sa’arsa a mazabar Daura, Mai’adua da Sandamu.

Mai girma gwamnan ya shawarci 'dan Buhari da kada ya rudu da sunan da mahaifinsa ya yi, ya yi kokarin gina nasa da kansa a harkar siyasa.

Dikko.
Gwamna Dikko Radda tare da wasu daga cikin iyalin Buhari da masu ruwa da tsakin APC na mazabar Daura, Mai'adua da Sandamu Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Yusuf ya ziyarci Sarkin Katsina

A nasa ɓangaren, Yusuf Buhari ya gode wa masu ruwa da tsakin da suka mara masa baya, yana mai cewa ba zai ba su kunya ba, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Bayan barin gidan gwamnatin Katsina, an ruwaito cewa Yusuf Buhari ta tawagarsa sun biya ta fadar Mai Martaba Sarkin Katsina, Abdulmuminu Kabir Usman domin neman aa albarkarsa kafin lokacin zaben fitar da dan takara na APC.

Kara karanta wannan

Bayan 'sallamar' mutum 2, an kara samun ministan da ya yi murabus a gwamnatin Tinubu

Yadda Yusuf Buhari ya amsa kira

A baya, an ji cewa dan marigayi Muhammadu Buhari, Yusuf ya and a kiraye-kirayen da ake yi masa na ya fito takarar dan Majalisar tarayya.

Ya aika da wasiƙar neman goyon baya ga jam'iyyar APC domin wakiltar mazaɓar Daura, Sandamu da Mai’Adua dake jihar Katsina a zaben 2027.

Yusuf Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babban burinsa shi ne kawo ayyukan raya ƙasa da kuma inganta rayuwar mutanen mazaɓarsa ta hanyar ilimi da sana'o'i.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262