Halin da Obi Ya Shiga da Rikici Ya Danno cikin Ƙungiyar Tafiyarsa da Kwankwaso

Halin da Obi Ya Shiga da Rikici Ya Danno cikin Ƙungiyar Tafiyarsa da Kwankwaso

  • Na kusa da Rabiu Musa Kwankwaso, Ladipo Johnson, ya ce da takarar jam'iyyar su ta NNPP ya shiga wani hali mara dadi
  • Ya ce Peter Obi bai ji daɗin rikicin shugabanci da ya kunno kai a cikin ƙungiyar OK da ke tallata shi da Kwankwaso ba
  • Ya bayyana rikicin a matsayin ɗan tangarda na wucin gadi da ba zai hana cimma burin siyasa da aka sako a gaba gabanin 2027 ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Ɗaya daga cikin makusantan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Ladipo Johnson, ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, bai ji daɗin rikicin shugabanci da ke addabar OK Movement ba.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ake samu raɗe-raɗin rashin jituwa a tafiyar da ke tallata Peter Obi da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso don zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

NNPP, NDC sun fara zazzafar musayar yawu game da takarar Obi da Kwankwaso

Kungiyar Obi Kwankwaso ta faɗa cikin rikici
Tsohon gwamna Peter Obi, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa kwankwaso
Source: Twitter

A ruwayar jaridar Vanguard, Johnson ya bayyana cewa tabbas akwai saɓani a cikin ƙungiyar mai don a kawo canjin shugabanci a Najeriya.

Rikici ya kunno kungiyar Obi da Kwankwaso

Daily Post ta kawo labarin cewa sai dai Ladipo Johnson ya jaddada cewa rikicin ba zai hana cimma manufofin siyasar ƙawancen Obi da Kwankwaso gabanin zaɓen 2027 ba.

A cewarsa, rikicin wata tangarda ce ta ɗan lokaci, don haka bai kamata ta zama sanadin rarrabuwar kawuna tsakanin magoya bayan ƙawancen ba.

A kalamansa:

"Eh, akwai abin da zan kira tangarda a wannan lokaci. A ra'ayina, ba irin wacce za ta sa mutum ya ɗauki matakin kai tsaye wanda zai iya rusa ko haddasa ƙiyayya tsakanin magoya bayan mutumin da kuke son ya zama shugaban ƙasar nan ba."

Johnson ya gargaɗi mambobin ƙungiyar da su guji duk wani mataki da zai raunana ƙoƙarin gina ƙaƙƙarfan dandamalin siyasa.

Obi/Kwankwaso: Abin da ya kawo rikici

Kara karanta wannan

APC ta yi wa gwamnan Osun barazana ana dab da zabe

Ɗaya daga cikin na hannun daman Kwankwason ya ce maimakon haka, ya kamata ya yi magoya baya su mayar da hankali wajen faɗaɗa tsarin ƙungiyar a sassan Najeriya.

Ya ce saɓanin ya samo asali ne daga rashin fahimta tsakanin wasu mambobi da shugabannin ƙungiyar, amma ya nuna kwarin gwiwar cewa za a iya warware matsalar.

Ladipo Johnson ya ce an sanar da Obi halin da ake ciki
Ladipo Johnson tare da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Johnson da ya bayyana kansa a matsayin kakakin Kwankwaso ya kuma bayyana cewa an riga an sanar da Peter Obi halin da ake ciki, kuma bai ji daɗin yadda lamarin ke tafiya ba.

Ya ce:

"Na gana da ɗan takarar shugaban ƙasa jiya da dare tare da Darakta Janar. Bai ji daɗin duk abin da ke faruwa ba."

Duk da rikicin, Johnson ya nace cewa bai kamata ya karkatar da hankalin magoya bayan ƙungiyar daga babban burinsu na gina ingantacciyar madadin siyasa ga Najeriya ba.

Ibrahim Muhammad, shugaban kungiyar Obidient reshen jihar Kano ya shaida wa Legit cewa wannan rikici ba zai kawo masu cikas ba.

Ya bayyana Legit cewa:

"Rikici ne na cikin gida, kuma a wannan tafiyar ta mu, ko Ok movement ko Obidient movement, akwai kyakkyawar alaka."

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su

Ya ce za a magance matsalolin ba tare da ya kawo naƙasu a cikin jam'iyyar ba ko tafiyarsu ta babban zaben 2027.

Ana musayar yawu kan Obi, Kwankwaso

A baya, mun kawo labarin cewa NNPP ta ce tsofaffin shugabanninta sun yi ƙoƙarin haɗa jam'iyyar da NDC domin goyon bayan Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a zaɓen 2027.

Sai dai jam'iyyar adawa ta NDC ta musanta zargin, tana mai cewa ba ta da wata yarjejeniya ko shirin haɗaka da NNPP kan batun takarar Kamar yadda ta ce ana nuna wa.

Yanzu haka, dukkannin bangarorin biyu sun ci gaba da musayar zarge-zarge kan rade-radin haɗakar siyasa kafin babban zaɓen 2027, inda NDC ta nemi NNPP ta kama alkiblarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng