A Wata 6 kacal, NNPCL Ya Saka fiye da Naira Tiriliyan 6 a Asusun Gwamnatin Tarayya

A Wata 6 kacal, NNPCL Ya Saka fiye da Naira Tiriliyan 6 a Asusun Gwamnatin Tarayya

  • NNPCL ya tura Naira tiriliyan 6.286 zuwa Asusun Tarayya tsakanin Janairu da Yunin 2026, ƙasa da rabin abin da ta biya a shekarar 2025
  • Kamfanin ya samu ribar Naira biliyan 535 a watan Yuni duk da ɗan raguwar yawan ɗanyen mai da aka haƙo
  • Ayyukan bututun iskar gas na OB3 da AKK sun kusa kammala, inda ake sa ran fara samar da iskar gas nan ba da jimawa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja - Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) ya tura Naira tiriliyan 6.286 zuwa Asusun Tarayya tsakanin watan Janairu da Yunin 2026, lamarin da ya tayar da fargabar cewa kuɗaɗen da zai biya gwamnati a bana na iya raguwa idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Rahoton kuɗi da ayyukan kamfanin na watan Yunin 2026 ya nuna cewa adadin ya kai kashi 42.7% kacal na Naira tiriliyan 14.706 da NNPC ta biya gwamnati a duk shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Malami ya bankado 'sirrin' Tinubu game da neman cin zabe ta kowace hanya

Kamfanin NNPCL ya sanya fiye da naira tiriliyan 6 a asusun tarayya a wata 6
Shugaban kamfanin NNPCL na kasa, Bashir Bayo Ojulari. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Kamfanin NNPCL ya samu ƙarin riba

Rahoton ya kuma nuna cewa NNPCL ya samu kuɗaɗen shiga na Naira tiriliyan 4.389 a watan Yuni, tare da ribar bayan haraji da ta kai Naira biliyan 535, in ji rahoton Daily Trust.

Wannan ya nuna ƙarin kashi 15.8% idan aka kwatanta da ribar Naira biliyan 462 da kamfanin ya samu a watan Mayu.

Sai dai rahoton ya bayyana cewa yawan ɗanyen mai da condensate da ake haƙowa ya ɗan ragu daga ganga miliyan 1.73 a rana a watan Mayu zuwa ganga miliyan 1.72 a watan Yuni.

Kamfanin ya danganta hakan da matsalolin ayyuka, lalacewar wasu cibiyoyin samar da mai da kuma wasu matsalolin fasaha a wuraren haƙar mai.

Manyan ayyukan iskar gas sun kusa kammala

NNPCL ya ce an samu gagarumin ci gaba a manyan ayyukan bututun iskar gas guda biyu da ake aiwatarwa a ƙasar.

Rahoton ya nuna cewa aikin bututun iskar gas na Obiafu-Obrikom-Oben (OB3) ya kai kashi 98% na kammalawa, yayin da ake shirin fara jigilar iskar gas a watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Atiku ya kalubalanci Tinubu kan sayo motocin alfarma a kan N15.13bn

NNPCL ya ce an samu gagarumin ci gaba a manyan ayyukan bututun iskar gas
Shugaban kamfanin NNPCL na kasa, Bayo Ojulari yana jawabi a wani taro. Hoto: @BBOjulari
Source: UGC

Haka kuma, aikin bututun iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK) ya kai kashi 94% na kammalawa, inda ake sa ran fara isar da iskar gas zuwa Abuja kafin ƙarshen wannan shekara.

A shekarar 2025, NNPCL ya samu kuɗaɗen shiga na Naira tiriliyan 60.5, ta samu ribar bayan haraji ta Naira tiriliyan 5.76, sannan ta tura Naira tiriliyan 14.706 ga gwamnatin tarayya a matsayin kuɗaɗen da doka ta tanada.

NNPCL ya tona abubuwa kan matatu

A wani labari, mun ruwaito cewa, shugaban NNPCL, Bayo Ojulari, ya bayyana cewa gwamnati ta yi asara sosai a wajen tafiyar da matatun man da ke hannunta.

Bayo Ojulari ya ce wannan babbar asara da ake tafka wa ta sa gwamnati ta yanke shawarar dakatar da ayyukansu domin hana ci gaba da salwantar da dukiyar ƙasa.

A cewarsa, babu laifi fushin da ‘yan Najeriya ke nunawa kan matatun man, la’akari da yawan kuɗin jama’a da aka zuba a cikinsu tsawon shekaru don a samu sauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com