Hare Haren Makiyaya: Abin da Tinubu Ya Fadawa Gwamnan Benue da Suka Hadu a Aso Villa
- Gwamna Hyacinth Alia ya gana da Shugaba Bola Tinubu da George Akume, domin nemo hanyar kawo karshen kisan da da ke yi Benue
- Alia ya ce shugabannin sun tattauna hanyoyin sulhu da hadin kai, don dawo da zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya a jihar
- Gwamnan ya musanta cewa gwamnatin tarayya ta ki taimaka masu, yana cewa goyon bayan da suka samu ne ya rage yawan hare-haren
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue – Gwamna Hyacinth Alia ya ce ya gana da Shugaba Bola Tinubu da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume kan halin da ake ciki a Benue.
Jihar Benue, wadda ke samar da abinci a yankin Arewa ta Tsakiya ta Najeriya, ta dade tana fama da munanan hare-hare daga wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne.

Asali: Facebook
Bola Tinubu ya gana da gwamna Hyacinth Alia
Gwamnan, wanda ya yi magana da gidan Talabijin na Channels, ya ce shugaban kasa ne da kansa ya kira taron domin nemo hanyar kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shafe tsawon shekaru ana irin wannan kisan, inda wasu ke danganta shi da rikice-rikice tsakanin garuruwa da kuma neman mamaye filaye a sassan jihar.
Sai dai, an shiga tashin hankali sosai a jihar sakamakon yadda 'yan ta'adda ke ci gaba da kai hare-hare sassa daban daban na jihar ba tare da tsagaita wuta ba.
Tinubu ya nemi a yi zaman sulhu a Benue
An tabbatar da mutuwar sama da mutane 160 a jerin hare-hare da ake zargin makiyaya ne suka kai, yayin da suka yi barna a cikin garuruwa daban-daban a jihar.
A ranar Lahadi, shugaban kasa ya umurci gwamnan da ya kira taron sulhu da tattaunawa tsakanin ɓangarorin da ke faɗa don kawo karshen zub da jinin da ake yi.
Hakazalika, Shugaba Tinubu na ganin cewa yin sulhu zai dawo da zaman lafiya mai ɗorewa da zaman tare mai inganci tsakanin manoma, makiyaya, da sauran mazauna jihar.
Alia ya yi magana bayan haduwarsa da Tinubu
A ranar Litinin, Gwamna Alia ya ce dole ne a magance rikice-rikicen da jihar ke fama da su ta hanyoyi daban-daban ciki har da sulhu.

Asali: Twitter
Ya kara da cewa:
"Za mu iya shawo kan rikicin da ke faruwa a cikin garuruwa da kuma tsakanin ƙananan hukumomi a jihar. Matsalar a nan ita ce baƙin da ke shigowa da makamansu na AK-47 da AK-49.
"Ina ganin shugaban ƙasa bai yi kuskure ba da ya ce mu yi amfani da hanyar sulhu. Ya gayyace ni da SGF saboda rade-radin da yake ji. Ya yi ƙoƙari ya gano ko akwai wani saɓani tsakaninmu.
"Sakataren gwamnatin tarayyar da kansa ya ce babu saɓani tsakaninmu. Idan ma akwai, a gaba ba za a samu damuwa ko kaɗan ba."
Alia ya kuma musanta iƙirarin cewa gwamnatin tarayya ba ta kai wa al'ummar jihar Benue dauki don kare su daga 'yan ta'addar da ke kashe su ba.
Mutane sama da 6,500 sun rasa muhalli a Benue
Tun da fari, mun ruwaito cewa, sojoji 2 da jami'in NSCDC ne aka ce sun mutu a harin kwanton bauna da 'yan bindiga suka kai masu a Benue.
Yayin da hare-haren Benue suka kara yawaita tare da jawo mutuwar sama da mutane 200, an ce mutane 6,527 ne suka rasa muhallansu a jihar.
A halin yanzu, NEMA ta ce tana hadaka da hukumomin SEMA, UNHCR, Red Cross da IOM domin tattara kayan agaji ga 'yan gudun hijira a Benue.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng