Gwamna Zulum Ya Zubar da Hawaye a Taron Nuna Goyon Baya ga Tinubu, An Ji Dalili

Gwamna Zulum Ya Zubar da Hawaye a Taron Nuna Goyon Baya ga Tinubu, An Ji Dalili

  • Gwamna Babagana Umara Zulum ya roki masu ruwa da tsakin APC da sauran al'ummar jihar Borno su masa afuwa idan ya bata masu
  • Zulum ya zubar da hawaye yayin da yake neman afuwa a taron APC da aka shirya domin jaddada goyon bayan tazarcen Tinubu/Shettima
  • Mai girma Gwamna Zulum ya bukaci ‘yan jam’iyyar su hada kai domin tabbatar da nasarar APC a babban zaben 2027 da ke tafe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya zubar da hawaye yayin da yake neman afuwar duk wanda ya bata wa rai a lokacin mulkinsa.

Gwamna Zulum ya yi wannan roko ne a wani taron manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Maiduguri a ranar Asabar, 25 ga watan Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan

'Kebbi taka ce': Gwamna ya yi alƙawari ga Tinubu, ya sha alwashi kan zaɓe

Zulum.
Gwamna Babagana Zulum a wurin taron masu ruwa da tsakin APC na jihar Borno Hoto: Abdurrahman Ahmed Bundi
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a yayin taron, shugabannin jam’iyyar APC a jihar Borno sun sake tabbatar da goyon bayansu ga tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima.

Goyon bayan tikitin Tinubu/Shettima

Mataimakin shugaban APC na kasa shiyyar Arewa, Hon. Ali Bukar Dalori, ne ya gabatar da kudirin amincewa da tazarcen Tinubu/Shettima, inda magoya bayan jam’iyyar suka amsa da babbar murya.

“Masu goyon bayan takarar Tinubu da Shettima su ce ‘Aye’,” inda dakin taron ya cika da amsa mai karfi.

Gwamna Zulum yana goyon-bayan Tinubu

Da yake jawabi, Farfesa Zulum ya jaddada cewa babu wani tikitin takara mafi alheri da ya kamata a mara wa baya kamar na Tinubu da Shettima.

Ya kuma bukaci ‘yan jam’iyya da masu ruwa da tsaki su fifita hadin kai da zaman lafiya yayin gudanar da harkokin siyasa a fadin jihar Borno.

“Mulki abu ne da Allah ke bayarwa ga wanda Ya so. Ko da mutum bai so wani ba, idan Allah Ya ba shi, zai samu,” in ji shi

Kara karanta wannan

Atiku, Kwankwaso da sauran 'yan adawa sun cimma matsayar da za ta girgiza Tinubu a 2027

Gwamnan ya bukaci ‘yan jam’iyyar su hada kai domin tabbatar da nasarar APC a babban zaben 2027

Zulum ya nemi afuwa a taron APC

Haka kuma ya tambayi wasu manyan jiga-jigan APC ciki har da mataimakinsa, Umar Kadafur, Sanata Mohammed Ndume, Ministan noma, Abubakar Kyari da Ali Bukar Dalori ko ya yi musu adalci a shekaru bakwai da suka gabata.

Dukkansu sun amince cewa ya yi wa al’ummar Borno adalci kuma ya kyautata a mulkinsa, amma duk da haka aka ga hawaye na zuba a idon Zulum.

Taron APC.
Masu ruwa da tsakin APC da suka halarci taron da aka shirya a gidan gwamnatin jihar Borno Hoto: Abdurrahman Ahmed Bundi
Source: Facebook

Shugaban APC na jihar, Bello Ayuba, ya ce ayyukan ci gaba da gwamnan ya aiwatar sun saukaka yakin neman zabe tare da jawo sababbin mambobi daga sauran jam’iyyu.

Ya kara da cewa akwai mutane da dama da suka sauya sheka zuwa APC, kuma suna jiran a karbe su a hukumance, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Gwamna Zulum ya zabi magaji a Borno?

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya bayyana cewa bai san wanda zai gaje shi ba bayan karewar wa’adinsa a watan Mayun 2027.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani

Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a watan Janairun 2026 yayin wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.

Zulum ya sanar da nasu ruwa da tsakin APC cewa bai tsaida dan takara ba kuma babu wani dan takara da yanke shawarar zai marawa baya a halin yanzu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262