Ana Zargin Ƴan Jagaliyar APC Sun Yi wa Mambobin PDP Jina Jina a Taron Sauya Sheƙa

Ana Zargin Ƴan Jagaliyar APC Sun Yi wa Mambobin PDP Jina Jina a Taron Sauya Sheƙa

  • Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari kan 'yan jarida da magoya bayan PDP a taron sauya sheƙar siyasa
  • Rahotanni sun ce akalla magoya bayan PDP 20 sun gamu da hari, takwas sun jikkata, yayin da aka lalata motoci, kujeru, rumfuna da sauran kayayyaki
  • PDP ta yi Allah wadai da harin, ta bukaci jami'an tsaro su binciki lamarin tare da hukunta masu hannu domin kare 'yancin siyasa da dimokuradiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abakaliki, Ebonyi - Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari kan 'yan jaridar a jihar Ebonyi yayin taron siyasa.

Majiyoyi suka ce an kuma kai hari kan mambobin jam'iyyar PDP yayin wani taron sauya sheka da aka gudanar a Idembia, karamar hukumar Ezza ta Kudu.

Kara karanta wannan

ADC ta bukaci Tinubu ya ceto daliban Borno kamar na Oyo

Yan APC sun lakadawa mambobin PDP duka
Taswirar jihar Ebonyi da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

'Yan jaridar sun je ne domin daukar rahoton sauya sheƙar tsohon jigon APC, Barista Ifeanyi Nworie, zuwa jam'iyyar PDP, cewar Punch.

Yawan wadanda aka kai masu hari a Ebonyi

Haka kuma, rahotanni sun ce akalla magoya bayan PDP 20 sun fuskanci hari, yayin da takwas daga cikinsu suka samu raunuka kuma ake kula da su a asibiti.

An ce wadanda suka kai harin sun haura mutum 100, kuma wani lauya da ke zaune a Abakaliki mai suna Mista Friday Agbom ne ya jagorance su.

An ce motar kungiyar 'yan jaridar mai tambarinta ta isa wurin katangar da ake zargin 'yan daban suka kafa yayin da suke kan hanyarsu zuwa sabon wurin taron da aka mayar bayan an tarwatsa wurin farko.

Rahotanni sun ce maharan sun rika bugun motar tare da kokarin bude kofofinta da karfi.

Direban motar ya tsere bayan an yi zargin wasu daga cikin maharan sun nemi fetur domin banka wa motar wuta.

Kara karanta wannan

An tsinci gawar malami a yashe, an ce wasu ne suka daɓa masa wuka har lahira

An kuma yi zargin cewa wani mutum da ake kyautata zaton magoyin bayan PDP ne ya sha duka a lokacin rikicin.

Bayan haka, Barista Nworie ya zargi cewa duk da sanar da rundunar 'yan sanda, DSS, NSCDC da sauran hukumomin tsaro kafin taron, har yanzu an samu wannan hari.

Ana zargin ƴan APC da kai hari kan ƴan PDP
Wani mamban PDP da ake zargin ƴan APC da Gwamna Francis Nwifuru. Hoto: Hon. Francis Nwifuru.
Source: Facebook

Martanin PDP a Ebonyi kan lamarin

Jam'iyyar PDP reshen Ebonyi ta yi Allah wadai da harin. Shugaban jam'iyyar, Mista Chukwuma Igwe, ya bayyana lamarin a matsayin hari kan dimokuradiyya, yana mai kira ga jami'an tsaro su kasance masu adalci yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Shi ma mataimakin shugaban PDP na kasa mai kula da yankin Kudu maso Gabas, Mista Chidiebere Egwu, ya ce abin takaici ne, yana jaddada cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowa damar shiga jam'iyyar siyasa da yake so.

Ya bukaci hukumomin tsaro su binciki lamarin tare da kamo da hukunta duk wadanda suka aikata wannan hari.

An yi wa dan APC suka kan Tinubu

An ji cewa Gwamnatin jihar Delta ta umarci jami'an tsaro su gano tare da kama mutanen da suka kai hari kan Simon Mudi, hadimin gwamna Sheriff Oborevwori.

Kara karanta wannan

An samu sababbin bayanai kan yadda aka sace shugaban karamar hukuma a Zamfara

An kai harin ne yayin taron masu ruwa da tsaki na APC a Delta ta Tsakiya, inda aka ji wa Simon Mudi da wasu raunuka masu tsanani.

Tsohon minista Solomon Dalung ya ce Simon Mudi na ci gaba da samun sauki, yana kuma godiya ga 'yan Najeriya da suka yi masa addu'a da nuna goyon baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.