El Rufai: DSS Ta Gurfanar da Tsohon Gwamnan Kaduna kan Zargin Leken Asiri
- A yau Alhamis, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja
- Hukuma DSS na zargin El-Rufai da laifuffuka biyar da suka shafi katsalandan da leken asiri kan tattaunawar wayar tarho ta NSA, Nuhu Ribadu
- Wannan takun-saƙa ya samo asali ne daga iƙirarin da El-Rufai ya yi a gidan talabijin cewa ya saurari umarnin da Ribadu ya bayar na a kama shi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Ana tuhumar El-Rufai da zargin kutse tare da sauraron tattaunawar wayar tarho ta Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.

Source: Twitter
DSS ta gurfanar da El-Rufai a kotu
A zaman kotun na ranar Alhamis, 23 ga watan Afrilu, 2026, lauyoyin gwamnati sun sanar da kotu cewa sun yi gyara a takardar karar daga tuhume tuhume uku zuwa guda biyar, in ji rahoton The Cable.
Bayan karanta masa tuhume-tuhumen, El-Rufai ya bayyana cewa bai aikata ko daya daga cikin dukkan tuhume tuhumen biyar ba.
Bayan El-Rufai ya musanta laifin, lauyan DSS, Oluwole Aladeloye, ya buƙaci kotu ta sa ranar fara shari'a.
Sai dai lauyan El-Rufai, Oluwole Iyamu, ya nuna rashin amincewa, inda ya bayyana cewa yana buƙatar lokaci domin tattaunawa da wanda yake karewa sakamakon ya shafe lokaci mai tsawo a hannun hukumomin tsaro daban-daban.
Takaddama kan batun belin El-Rufai
Lauyan na El-Rufai ya kuma nuna fushinsa kan yadda aka gaza sauraron buƙatar neman belin tsohon gwamnan.
Sai dai Alkalin kotun, Joyce Abdulmalik, ta soki lauyan inda ta bayyana cewa wasu takardun karin bayani da yake iƙirarin ya shigar ba su iso gare ta ba.

Kara karanta wannan
Kotu ta dauki matakin farko kan wadanda ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki
Ta gargaɗi lauyan da ya daina yin abin da ta kira "wasan kwaikwayo na Nollywood" a cikin kotu tare da masu ɗaukar hoto, in ji rahoton Daily Trust.

Source: UGC
Dalilin DSS na gurfanar da El-Rufai
Wannan shari'a ta samo asali ne daga wata hira da El-Rufai ya yi da gidan talabijin na Arise TV a watan Fabrairun da ya gabata.
A lokacin hirar, El-Rufai ya fito fili ya bayyana cewa wani ya yi kutse a wayar Nuhu Ribadu, wanda hakan ya ba shi damar sauraron lokacin da Ribadu yake ba jami'an tsaro umarnin su kama shi.
A lokacin, El-Rufai ya bayyana cewa:
"Gwamnati tana tsammanin ita ce kaɗai ke sauraron kiran waya, amma mu ma muna da namu hanyoyin. Wani ya yi kutse a wayarsa kuma ya shaida mana cewa ya bayar da umarnin a kama mu."
Waɗannan kalamai ne suka sa hukumomin tsaro suka shiga bincike har aka kai ga gurfanar da shi.
DSS ta cafke El-Rufai
Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, hukumar DSS ta kama tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, jim kaɗan bayan EFCC ta sake shi daga rikon kwanaki biyu da ta yi masa.

Kara karanta wannan
Kurunkus: An gurfanar da mutane 6 da ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki a Najeriya
Malam Nasir El-Rufai ya kasance a hannun EFCC tun ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026 kan zargin almundahanar kuɗaɗe, inda aka ba da shi beli da misalin ƙarfe 8:00 na dare.
Kama El-Rufai da DSS ta yi yana da alaƙa da zargin cewa ya sa an riƙa sauraren tattaunawar wayar NSA, Nuhu Ribadu, ba tare da izini ba.
Asali: Legit.ng
