Rashin kasancewar Shugaban Kamaru Paul Biya har na kwanaki 48 ya rura wutar mahawara tsakanin 'yan adawa kan samun gurbin shugabanci da rikicin makusantansa.
Rashin kasancewar Shugaban Kamaru Paul Biya har na kwanaki 48 ya rura wutar mahawara tsakanin 'yan adawa kan samun gurbin shugabanci da rikicin makusantansa.
'Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukumar Bungudu a Zamfara bayan sun kashe jami'an tsaro huɗu. Jami'ai sun ceto wasu daga cikin 'ya'yansa yayin artabun.
Wani mutum ya nuna kaduwarsa kan farashin da ya siya man fetur a jihar Enugu. Mutumin ya nuna shaida sannan ya bayyana sunan gidan man da ya siye shi kan haka.
Yayin da ake ci gaba da shari'ar matashiyar 'yar Tiktok a jihar Kano, Murja Ibrahim Kunya, Kotun Shari'ar Musulunci ta sake hukunci kan zarginta da ake yi.
Wani bidiyo da ya yadu wanda aka ce an dauke shi a bidiyo ne ya nuno tarin wayoyi da wasu mambobin coci suka jona. Bidiyon ya haifar da martani a soshiyal midiya.
Da alamu abubuwa za su yi sauki yayin da farashin kayayyaki musamman na abinci ya fara sauka a wasu kasuwannin Arewacin Najeriya yayin da ake cikin wani hali.
Dr Emmanuel Iwuanyanwu, shugaban Ohanaeze Ndigbo, ya gargadi Inyamurai a fadin kasar kan shiga zanga-zanga kan matsin rayuwar da ake ciki karkashin Tinubu.
An yi ta zanga-zanga a fadin Najeriya tun bayan cire tallafin mai da kuma tsare-tsaren da Tinubu ya kawo a bangaren daidaita naira ya kefa mutane cikin wani hali.
AEDC yana barazanar yanke wutan Aso Villa, barikin sojoji saboda rashin biyan kudin wutar lantarki. Daga yanzu zuwa 28 ga Fubrairu ake bukatar a biya duk wani bashi.
Wani matashi ‘dan Najeriya ya garzaya dandalin soshiyal midiya don fallasa abokinsa da ya kama yana shan garin kwaki da man ja. Nan take matashin ya boye abincin.
A lokacin da ake neman abinci a Najeriya, sai ga motoci za su tsallaka Nijar. Mai magana da yawun bakin hukumar ZARTO a Zamfara ya tabbatar da wannan zance.
Labarai
Samu kari