Rashin Wuta: Yadda Wajen Ibada Ya Zama Matattarar Cajin Wayoyi, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Rashin Wuta: Yadda Wajen Ibada Ya Zama Matattarar Cajin Wayoyi, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • Wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya ya nuno tarin wayoyi da sauran kayan wuta suna caji a wani wurin bauta da aka ce coci ne
  • Wayoyin da kayan wutan sun yi yawa matuka lamarin da ya sanya mutane tambayar ko da gaske wajen coci ne ko kuma wurin caji
  • Wasu masu amfani da dandalin TikTok da suka ga bidiyon sun bayyana cewa wajen ya yi kama da wajen daukar darasi maimakon coci

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani bidiyo da ke yawo a dandalin soshiyal midiya ya nuno wayoyi masu yawan gaske da aka jona jikin caji a wani wuri da aka ce coci ne.

A cewar @dahcutemide0, wacce ta wallafa bidiyon a TikTok, an dauki bidiyon ne a jami'ar Olabisi Onabanjo.

Kara karanta wannan

Ana karbar kebura: Bidiyon wani matashi da ke shan garin kwaki da man ja ya girgiza intanet

Ta ce mutane na kawo wayoyi coci don yin caji
Rashin Wuta: Yadda Wajen Ibada Ya Zama Matattarar Cajin Wayoyi, Bidiyon Ya Girgiza Intanet Hoto: TikTok/@dahcutemide0.
Asali: TikTok

A 'dan gajeren bidiyon, an gano wayoyi da sauran kayan wuta da dama makale a jikin caji a wani lungu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wayoyin suna da yawa ta yadda wasu 'yan TikTok da suka ga bidiyon suke kokwanto cewa wajen bai yi kama da coci ba.

Wasu sun yi martani mai ban dariya, cewa suma suna so su zo cajin wayoyinsu yayin da ake fama da matsalar wuta a kasar.

An yi wa bidiyon take da:

"Waya kowa ya je caji a coci."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani yayin da mutane suka je caji a coci

@X_cite ta yi martani:

"Wayoyi sun fi mambobin cocin yawa."

@Hajia Shattia ta yi martani:

"Allah ya albarkaci Ghana koda a iya wutar lantarki ne."

@Abimbola Arike ta ce:

"Abu mafi muni shine ace wani joni daya ya gauce sauran. Za a sha kuka ba na wasa ba."

Kara karanta wannan

Tsadar siminti: Yadda wasu maza 2 suka dukufa ginin gida babu siminti, bidiyon ya haddasa cece-kuce

@R ya ce:

"Kai suna da karfin hali faa. Ina da matsalar yarda."

@Ms.Dandy ta yi martani:

"Wayoyi sun fi 'yan coci yawa."

Kamfanonin wuta sun zalunci 'yan Najeriya

A wani labari na daban, an rahoto cewa kamfanonin raba wuta na DisCos suna zaluntar abokan huldarsu.

Wani bincike da aka gudanar ya nuna kamfanonin sun karbi kudin wuta da ya kere hakkokinsu a wajen al'ummar kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel