Kudin Lantarki: Za a Shiga Duhu, Ana Bin Fadar Aso Rock da Ma'aikatu Bashin N47bn

Kudin Lantarki: Za a Shiga Duhu, Ana Bin Fadar Aso Rock da Ma'aikatu Bashin N47bn

  • AEDC masu raba lantarki a Abuja sun fitar da sanarwa game da wadanda ake bi tsohon bashin wuta sun gagara biya
  • Idan aka kai karshen watan Fubrairun nan ba a biya kudin lantarkin da aka sha ba, sanarwar tace za a datse masu wuta
  • Kamfanin AEDC ya biyo fadar shugaban kasa, gwamnan CBN, gwamnatin Neja da wasu ma’aikatu bashin kusan N50bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kamfanin AEDC masu raba wutar lantarki a kewayen garin Abuja sun bada wa’adin kwanaki goma su yanke wuta a wurare.

A ranar Litinin AEDC ya fitar da sanarwa a jaridu zai yanke wutan hukumomi, ma’aikatu da cibiyoyin gwamnati bayan karin kudi.

Lantarki
AEDC zai yanke wutar lantarki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ma'ikatu 86 ba su biya kudin lantarki ba

Kara karanta wannan

An maida motocin abinci 50 Najeriya, za su shiga kasar Nijar bayan umarnin Tinubu

Kamfanin lantarkin ya sanar da cewa yana bin wadannan ma’aikatu 86 bashin N47.1bn, rahoton Premium Times ya tabbatar da hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwa da aka fitar, AEDC ya nuna dole ta sa ya tona asirin abokanan huldarsu.

Kamfanin na DisCos ya ce har zuwa Disamban 2023, wadannan ma’aikata sun gaza biyan bashin kudin da ake bin su na wutan da suka sha.

Lantarki: Jawabin kamfanin AEDC

"An tilastawa kamfanin raba wutar lantarkin Abuja (AEDC), ya fitar da wannan sanarwa dauke da bayanan hukumomi da ma’aikatun gwamnati da ke da tsofaffin bashin wutar lantarkin da suka sha"
"A baya, yunkurinmu na ganin sun sun sauke nauyin da ke wuyansu bai yi nasara ba."

- AEDC

Su wanene a gaba a bashin shan lantarki?

The Cable ta ce daga sanarwar an fahimci ana bin fadar shugaban kasa bashin N923.87m duk da kudin da aka ware a gyaran Aso Rock.

Kara karanta wannan

An cafke mutane 5 da ‘sace’ buhuna 1800 na abincin ‘yan gudun hijira a Kano

Akwai bashin N12bn a kan barikin shugaban hafsun sojoji da sauran ofisoshin sojoji, ana bin ma’aikatar harkokin birnin Abuja bashin N7.5bn.

Kamfanin ya ce ma’aikatar kudi za ta biya shi N5.4bn sannan an sake biyo gwamnatin Neja bashin N3.4bn, sai CBN yana da N1.58bn.

Daga yanzu zuwa 28 ga Fubrairu ake bukatar a biya duk wani bashi ko AEDC su yanke wuta a lokacin da ake maganar janye tsarin tallafi.

Cire tallafin fetur da lantarki

An ji labari ana zargin an cigaba da biyan tallafin da Bola Tinubu ya yi ikirarin ya cire a kan man fetur a ranar da ya zama sabon shugaban kasa.

Masana a hukumar IMF sun zargi Gwamnatin tarayya da biyan kudi domin a hana fetur tashi, suna so a janye tallafi har a kudin sayen lantarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel