Kano: Wata kungiya Ta Sake Tura Wasika Majalisa Kan Fasalin Masarautun Jihar, Ta Tura Gargadi

Kano: Wata kungiya Ta Sake Tura Wasika Majalisa Kan Fasalin Masarautun Jihar, Ta Tura Gargadi

  • Wata kungiya a Kano ta sake tura wasika zuwa ga Majalisar jihar kan sake fasalin masarautun da ake tababa a kansu
  • Kungiyar mai suna Inuwar Masarautar Bichi ta yi gargadi ne kan mayar da masarautun daga biyar zuwa daya da ake fada
  • Wannan na zuwa ne bayan kungiyar 'Yan Dangwalen Kano ta bukaci a sake fasalin masarautun jihar din da mayar da Sunusi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake ta kiran gyaran fuska a masarautun Kano, wata kungiya ta gargadi Majalisar jihar kan hakan.

Kungiyar mai suna Inuwar Masarautar Bichi ta yi gargadi ne kan mayar da masarautun daga biyar zuwa daya da ake fada.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta sake ba da sabon umarni ga likitoci kan 'yar Tiktok, Murja, ta fadi dalili

Kungiya ta tura gargadi ga Majalisar Kano kan masarautun Kano
Kungiya ta gargadi Majalisa kan taba masarautun Kano. Sunusi Lamido, Abba Kabir.
Asali: Original

Wane gargadi kungiyar ta tura ga Majalisar a Kano?

Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika da kungiyar ta tura ga kakakin Majalisar kan tarwatsa masarautun, kamar yadda Leadership ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar:

"A kwanakin nan an yaɗa a kafafen sadarwa kan wata kungiya mai suna 'Yan Dangwalen Kano ta tura bukata zuwa Majalisa kan batun masarautu.
"Kungiyar ta na bukatar Majlisa ta sake fasalin masarautun wurin mayar da su guda daya da aka kirkira zuwa biyar."

Shawarar da kungiyar ta bayar kan masarautun Kano

Kungiyar ta ce idan aka bi umarnin 'Yan Dangwalen Kano hakan zai zama barazana ga masarautar Bichi da sauran masarautun.

Har ila yau, ta ce sake mayar da masarautun zuwa guda daya zai tarwatsa zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake da shi.

Daga bisani ta bukaci Majalisar ta yi watsi da bukatar 'Yan Dangwalen Kano da duk wasu bukatu makamancin haka cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da shari'ar Murja Kunya

Ta kara da cewa:

"Muna kira ga Majalisar da ta duba zaman lafiyar jihar wanda kin hakan zai kawo cikas tun da mutane su na son sarakunan da masarautun a haka."

Kungiyar ta tura sako Majalisa

Kun ji cewa 'Yan Dangwalen Kano sun bukaci Majalisar jihar Kano ta sake duba fasalin masarautun jihar don samun zaman lafiya.

Kungiyar ta tura bukatar ce da kuma neman mayar da tsohon Sarki Sunusi Lamido Sunusi kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel