Boka Ya Fito Yana Yi wa ADC Kulle Kulle, Gwamnan Sokoto Ya Magantu
- Gwamnatin jihar Sokoto ta nesanta kanta da wani bidiyon wani boka da ake kira Mai Shaho da ya yaɗu a kafafen sada zumunta yana aikata tsafi
- Gwamnatin ta ce ba ta da wata alaƙa da mutumin ko ayyukansa, tare da jaddada cewa ba ta goyon bayan masu tsafi ko masu sihiri
- Haka kuma ta bukaci Hukumar Hisbah ta jihar da ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wani aiki da ya saɓa wa koyarwar addinin Musulunci da dokokin ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Gwamnatin jihar Sokoto ta fito karara ta nesanta kanta da ayyukan wani boka da aka fi sani da Mai Shaho, bayan wani bidiyonsa ya bazu a kafafen sada zumunta.
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na gidan gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar a ranar 24 ga Yulin 2026, gwamnatin ta ce ba ta da wata alaƙa da mutumin ko ayyukan da yake yi.

Source: Facebook
Sanarwar da aka fitar a Facebook ta zo ne bayan wani bidiyo ya nuna mutumin yana birne akuya da ranta, tare da ikirarin cewa wani ɗan takarar gwamna na wata jam'iyyar siyasa a jihar ba zai samu karɓuwa daga masu zaɓe ba.
Maganar gwamnatin Sokoto
A sanarwar da ta fitar, gwamnatin ta bayyana cewa ba ta goyon bayan ayyukan masu tsafi ko masu sihiri ko waye shi.
Ta ce ba ta da hannu a duk abin da aka gani a cikin bidiyon, kuma ba za ta lamunci duk wani aiki da ya saɓa wa dokoki, al'adun jama'a da kuma koyarwar addinin Musulunci ba.
A cewar sanarwar, al'ummar jihar Sokoto galibi Musulmai ne, kuma suna bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW), sahabbansa da kuma tafarkin Mujaddadi Sheikh Usmanu Ɗanfodiyo.
An nemi Hisbah ta ɗauki mataki
Gwamnatin ta shawarci duk masu aikata ayyukan da suka saɓa wa ingantacciyar koyarwar Musulunci da su daina nan take.
Haka kuma ta yi kira ga Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto da ta ɗauki matakin da ya dace bisa tanadin doka domin dakile irin waɗannan ayyuka.
Sanarwar ta jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta amince da duk wani abu da zai saɓa wa addini, doka da kuma martabar al'ummar Sokoto ba.

Source: Original
Maganar wani dan Sokoto
Kafin fitar da sanarwar gwamnatin, wani mai amfani da Facebook mai suna Haruna Sambo Wali da ya wallafa bidiyon ya buƙaci gwamnatin jihar da ta fito fili ta barranta kanta daga Mai Shaho.
Ya ce abin takaici ne a riƙa aikata irin waɗannan abubuwa a jihar Sokoto, yana mai cewa irin waɗannan ayyuka ne Mujaddadi Sheikh Usmanu Ɗanfodiyo ya yaƙa a ƙasar Hausa.
Haruna ya kuma buƙaci gwamnati ta ɗauki matakin doka kan mutumin, yana mai zargin cewa an ambaci sunan ɗan takarar gwamnan jam'iyyar ADC a cikin bidiyon da ake yaɗawa.
An ba da hutu a Sokoto
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Sokoto ta ayyana ranar Juma'a, 24 ga Yuli, 2026, a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan gwamnati domin su samu damar yin rajistar katin zaɓe.
Gwamna Ahmed Aliyu ya bukaci ma'aikatan da ba su yi rajista ba su yi amfani da wannan dama wajen kammala rajistar masu zaɓe da karɓar katin PVC.
Ya kuma ƙarfafi sauran al'ummar jihar da suka cancanci yin rajista da su yi amfani da ƙarin makonni biyu da INEC ta bayar domin yin rajista.
Asali: Legit.ng


