Tsadar Rayuwa: Talakawa Na Murna Yayin da Farashin Abinci Ya Fara Sauka a Kano da Wasu Jihohin Arewa

Tsadar Rayuwa: Talakawa Na Murna Yayin da Farashin Abinci Ya Fara Sauka a Kano da Wasu Jihohin Arewa

  • Da alamu farashin kayayyaki ya fara sauka a wasu kasuwannin Arewacin Najeriya yayin da ake cikin wani hali
  • A jihohin Taraba da Kano da Kwara da kuma Neja farashin ya sauka idan aka kwatanta da makon da ya gabata
  • Wannan na zuwa ne bayan zanga-zanga a jihohin Kano da Neja da Legas kan tsadar kayayyaki a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Yayin da ake kuka kan halin tsadar abinci a Najeriya, da alamu a wasu wurare hakan ya fara sauki.

Farashin kayan abinci ya fara sauka musamman a wasu kasuwannin hatsi a jihohin Kano da Taraba da kuma Neja, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kano da sauran jihohi 3 da aka gudanar da mummunar zanga-zanga a Najeriya

Farashin abinci ya fara sauka a wasu jihohin Arewacin Najeriya
Da alamu sauki ya zo yayin da farashin abinci ya fara sauka. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Twitter

An yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa

Idan ba manta ba an samu zanga-zanga a jihohin Kano da Neja da Legas kan tsadar kayayyaki a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin matakai da aka dauka ana tunanin sune silar fara saukar farashin kamar hana fitar da abincin a wasu jihohi.

Sauran sun hada da kai samame kan wasu da ake zargin su na boye abinci don ya yi tsada da kuma saka ido a iyakoki.

Yanayin farashin kayan abinci a kasuwanni

Misali a jihar Kano farashin masara da wake da shinkafa da kuma waken suya sun zube a kasuwanni, cewar VON.

A wasu wurare ana siyar da buhun masara dubu 48 zuwa 50 sabanin dubu 58 zuwa 60 a makon jiya yayin da wake ya fadi zuwa dubu 85 daga dubu 94.

Kara karanta wannan

An maida motocin abinci 50 Najeriya, za su shiga kasar Nijar bayan umarnin Tinubu

Masara da shinkafa da wake da na suya sun fara sauka a kasuwannin Doguwa da Tudun Wada da Bunkure da sauransu.

Wani dan kasuwa a Bunkure, Adam Isah ya ce faduwar kayan na da alaka da rashin yawan neman kayan da ake yi.

A jihar Taraba, wani manomi a Maihula, Ali Maihula ya fadawa Daily Trust cewa masara ta zube daga dubu 54 zuwa 40 yayin da waken suya ta zube daga dubu 40 zuwa 32.

Inda aka tabbatar kayan sun sauka akwai kasuwannin Mutum Biyu da Garba-Chede da Maihula da Iware

A Bida da ke jihar Neja an tabbatar da cewa farashin masara ya zube daga dubu 52 zuwa 48 yayin da dawa ta sauko zuwa dubu 39 daga 58.

A jihar Kwara buhun masara da ake siyarwa a dubu 65 ya dawo dubu 40 a jiya yayin da wake da ake siyarwa dubu 100 ya dawo dubu 90.

Kara karanta wannan

Jerin jihohin Najeriya 10 da aka fi samun kayan abinci da tsada, Kogi na kan gaba

Majalisa ta yi alkawari ga ‘yan kasa

Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta yi alkawari ba za ta bari a kara kudin wuta da na man fetur ba a kasar.

Wannan na zuwa ne yayin da ake hasashen cire tallafin wutar lantarki a Najeriya bayan na man fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel