Abba Zai Sallami Mutane 1300 da Aikin Titi Ya Biyo ta Wurarensu a Jihar Kano

Abba Zai Sallami Mutane 1300 da Aikin Titi Ya Biyo ta Wurarensu a Jihar Kano

Akwai mutane da yawa da ayyukan tituna ko samar da ruwa ya jawo gwamnati ta taba filayensu a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Za a biya mutane sama da 1,400 kudin diyya kai tsaye ta asusun bankunansu tunda an shiga hakkokinsu

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kinkimo ayyukan bunkasa rayuwa na zamantar da birnin Kano

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta amince da biyan kudi domin sallamar wadanda ayyukan tituna da za a yi ya biyo ta wurinsu.

Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da wannan a zama na 40 da aka yi wanda Mai girma Abba Kabir Yusuf ya jagoranta.

Abba kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf da wani wuri da ake aikin hanya a Kano Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

Gwamnatin Abba tana ayyukan tituna a Kano

A sakamakon fadada tituna a garin Kano, za a taba wuraren wasu mutane, Daily Trust ta kawo rahoton a cikin karshen makon nan.

Kara karanta wannan

Boka ya fito yana yi wa ADC kulle kulle, gwamnan Sokoto ya magantu

Mutanen da gwamnatin Abba Yusuf za ta sallama sun kai 1, 400 lokacin da aka amince da manyan ayyuka da tsare-tsare a fadin Kano.

Kwamishoni da sauran ‘yan majalisar zartarwa sun yi na’am da ayyukan na sama da Naira biliyan 55 da gwamnati za ta yi wa jama’a.

Daga cikin wadannan ayyuka ne aka ware N3.1bn a sallami mutane 361 da za a taba wurare a wajen gina titin Kano Northern Bypass.

Za a biya mutanen Kano hakkokinsu

A baya an ji yadda wasu suka rika kira ga gwamnati ta biya kudi ga duk mutanen da ayyukan tituna ko ruwa zai ci kadarorinsu a Kano.

Masana tarihi sun ce an yi irin haka bayan gwamnatin soja ta ci filayen mutane a shekarun baya, Legit Hausa ba ta da tabbacin hakan.

A farkon zuwan gwamnati mai-ci a Mayun 2023, ta rushe gidaje, gine-gine da shuguna rututu.

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a ofishinsa Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

Gwamnati za ta sallami mutanen Gaya, Kura & Gwarzo

Abin bai tsaya nan ba, akwai N2.9bn da aka amince za a batar a kan mutane 1, 113 da za a taba wa dukiya wajen fadada titi a Gaya.

Kara karanta wannan

An bayyana yadda Yariman Saudiyya Abdullah bin Fahad ya rasu a otal din Landan

Gwamnatin Kano tana kokarin fadada titi mai tsawon kilomita biyar a karamar hukumar Gaya.

Bayan nan kuma akwai hanyar Kano–Dawakin Tofa–Gwarzo–Dayi da ita ma ake fadada ta, an ware wa mutane N247m saboda hakan.

Manoma da aikin ruwan Tamburawa zai shafa a karamar hukumar Kura za su samu N213.7m saboda rasa bishiyoyi da gonakinsu.

Rahoton ya ce gwamnati ta amince da biyan wadannan biliyoyin kudi ne ta karkashin ma’aikatar filaye da tsare-tsaren birni ta Kano.

Ana sa ran idan aka yi hakan, ‘yan kwangila za su iya kammala ayyukan cikin sauki ba tare da mutanen garuruwa sun yi korafi ba.

APC tana yi wa Kwankwaso barna a Kano

Labari ya gabata game da yadda APC ta ci burin raba Rabiu Musa Kwankwaso da NDC da Sanata Rufai Hanga da Kabiru I. Gaya.

Shugaban APC na kasa da kan shi ya ziyarci wadannan manyan 'yan siyasa ganin cewa ba su samu takarar sanatoci a jam'iyyar NDC ba.

Watakila sai inda karfin shugabannin APC ya kare wajen karya kashin bayan jam'iyyar NDC a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng