An Bankado Wani Muhimmin Sirri na Sojojin da Ake Zargin da Kifar da Gwamnati

An Bankado Wani Muhimmin Sirri na Sojojin da Ake Zargin da Kifar da Gwamnati

  • Wasu takardun bincike sama da shafuka 7,400 sun bayyana cikakken shirin da ake zargin wasu jami'an soja a juyin mulki
  • Ana zargin masu shirin sun raba ayyuka tsakanin jami'ai, suka yi amfani da kalmomin sirri, tare da tsara komai
  • Takardun sun kuma nuna an shirya dakatar da zirga-zirgar jiragen sama, tattara sojoji da makamai, tare da kafa tsarin mulki na rikon kwarya bayan karbe iko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sababbin bayanai sun fito kan abin da ake zargin shi ne cikakken tsarin wasu jami'an soja kan juyin mulki.

An ce jami'an sun tsara abubuwa domin tsara domin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a bara.

An gano wasu bayanai kan yunkurin juyin mulki
Wanda ake zargi da kitsa juyin mulki, Kanal Ma'aji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Yadda aka tsara juyin mulkin Tinubu

Takardun bincike da Premium Times ta samu sun bayyana yadda aka raba ayyuka, aka tsara ranakun aiki cikin sirri, aka yi amfani da kalmomin sirri, tare da tsara yadda za a gudanar da sauyin mulki.

Kara karanta wannan

Matar aure ta kwarawa kishiyarta mai ciki ruwan zafi, ta haihu dan ya mutu

Bayanan sirri a takardun sama da shafuka 7,400 sun kunshi bayanan da wadanda ake zargi suka bayar wa masu bincike, bayanan asusun banki, rubuce-rubucen sirri, hujjojin tattaunawa da sauran shaidu.

Binciken ya nuna cewa shirin ya mayar da hankali kan kwace muhimman sansanonin soja, cibiyoyin watsa labarai, tara sojoji da kuma dakile manyan hafsoshin rundunonin tsaro.

Rahotannin baya sun bayyana cewa Kanal Mohammed Ma'aji ne ake zargin ya jagoranci shirin tare da Kanal mai ritaya M.M. Adamu, Laftanar Kanal Shamsuddeen Bappah da Manjo Abdulkarim Ibrahim.

Ana zargin dukansu, ban da M.M. Adamu da ake cewa har yanzu yana gudun hijira, sun bayar da bayanai masu kama da juna ga masu bincike.

Ana ci gaba da bincike kan yunkurin juyin mulkin Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Kitsa kai hari fadar shugaban kasa

Ana zargin an dora wa wani mai suna Usman alhakin jagorantar farmaki kan Fadar Shugaban Kasa bayan ya gudanar da binciken sirri tare da taimakon wasu jami'ai da suka hada da dan sanda Ahmed Ibrahim.

A zaman shari'ar da ake yi a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, masu gabatar da kara sun nuna bidiyo inda Zekeri Umoru ya ce masu shirin sun tattauna yiwuwar kashe wutar lantarki ta Fadar Shugaban Kasa lokacin fara aikin.

Kara karanta wannan

Kasar Isra'ila ta kai hare hare Gaza, ta kashe Falasdinawa

Sai dai ya ce ya gargade su cewa hakan zai jawo bincike da kama ma'aikatan da ke bakin aiki.

Ana zargin masu shirin juyin mulki sun yi imanin cewa dole ne a dakatar da tashin da saukar jiragen sama domin shirin ya yi nasara.

A cewar bayanan masu bincike, an shirya amfani da motar bindiga a filin jirgin Abuja domin dakatar da zirga-zirgar jirage.

Haka kuma wani Laftanar mai suna Sunday Felix ya ce an ba shi aikin tattara bayanai kan filin jirgin Legas da kuma yadda za a dakile ayyukansa a ranar da za a fara shirin.

Takardun sun kara nuna cewa ana zargin masu shirin sun tsara tara sojoji, motoci, makamai da alburusai daga bataliyoyi daban-daban.

Wasu jami'ai sun ce sun tabbatar suna da isassun sojoji da kayan aiki, duk da cewa ba a sanar da su ranar fara aiwatar da shirin ba.

Har ila yau, wani da ake zargi mai suna Bayawo Abdullahi ya ce an ba shi aikin tattara jami'ai daga rundunar ruwa da yake jagoranta.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: An yanke wa mutum 3 hukuncin daurin rai da rai kan sace daliban Oyo

Ya ce yana da sojoji 14 a karkashinsa tare da motocin Hilux guda uku da za a iya amfani da su wajen gudanar da aikin.

Juyin mulki: Gwamnatin Tinubu ta kawo shaidu 30

Mun ba ku labarin cewa Kotun Tarayya da ke Abuja za ta saurari shari’ar wasu mutane shida da ake zargi da shirya juyin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Gwamnatin tarayya ta gabatar da jerin shaidu 30 da suka hada da jami’an bincike, masana fasahar bincike da jami’an bankuna.

Masu gabatar da kara sun ce za su gabatar da takardu, bayanan banki da na’urorin sadarwa domin tabbatar da zarge-zargen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.