Tsadar Rayuwa: Kano da Sauran Jihohi 3 da Aka Gudanar da Mummunar Zanga-Zanga a Najeriya

Tsadar Rayuwa: Kano da Sauran Jihohi 3 da Aka Gudanar da Mummunar Zanga-Zanga a Najeriya

Yan Najeriya da dama na cikin mawuyacin hali bayan tsare-tsaren tattalin arziki da Shugaba Tinubu ya aiwatar a kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Tun bayan cire tallafin mai da kuma tsarin da Tinubu ya kawo a bangaren daga darajar naira duk ya jefa mutane cikin wani hali.

Jerin jihohin Najeriya 4 da aka gudanar da zanga-zanga
Tsadar rayuwa ta janyo barkewar zanga-zanga a wasu jihohin Najeriya. Hoto: Bola Tinubu, Concerned Nigeria.
Asali: Twitter

Farashin kaya musamman na abinci ya ninka wanda aka sani a baya inda mutane ke korafin irin halin kunci da ake ciki.

Hausa Legit ta jero muku jihohin da aka gudanar da zanga-zanga kan mawuyacin hali da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Kano

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Bayan Kano da Minna, sabuwar zanga-zanga ta barke a wata jihar Kudu

Cibiyar kasuwanci na daga cikin jihohin da aka gudanar da zanga-zanga kan matsanancin halin kunci da ake ciki, cewar Vanguard.

Mata da matasa da kuma dattawa ne suka fito don nuna rashin jin dadinsu kan tsadar abubuwa inda daga bisani gwamnati ta kulle wasu shaguna da ake zargin su na boye abinci.

2. Neja

Wasu ‘yan Najeriya sun barke da zanga-zanga a jihar Neja kan halin kunci inda suka bukaci Tinubu ya kawo dauki.

Jihar Neja makwabciyar birnin Tarayya ce Abuja inda aka gudanar da zanga-zangar don nuna damuwa kan halin da ake ciki.

3. Oyo

A ranar 19 ga watan Faburairu ce matasa suka taru a yankin Mokola da ke Ibadan suka fantsama zanga-zanga kan halin kunci da ake ciki.

Matasan sun yi ta wake-wake don nuna damuwa kan mawuyacin hali da ‘yan kasar ke ciki.

4. Cross River

Ma’aikata a jihar Cross River sun barke da zanga-zanga kan halin kunci da kuma rashin biyan albashi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kona mutane 12 har lahira, sun kuma babbake gidaje 17 a wata jihar Arewa

Ma’aikatan sun koka kan halin yunwa da ake ciki inda suka ce har zuwa ranar 15 ga watan Faburairu ba a biya albashi ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an gudanar da zanga-zangar ce a ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Cross River.

Majalisa ta yi alkawari ga ‘yan kasa

A baya, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta yi alkawarin tsayawa ‘yan Najeriya kan halin da ake ciki.

Majalisar ta ce ba za ta taba bari a kara farashin man fetur da wutar lantarki ba a kasar yayin ake cikin wani hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel