An Kashe Iyalan Fasto a Filato, Amurka Ta Yi Gargadi Kwana 1 bayan Yabon Tinubu

An Kashe Iyalan Fasto a Filato, Amurka Ta Yi Gargadi Kwana 1 bayan Yabon Tinubu

  • Gwamnatin Amurka ta yi Allah-wadai da mummunan kisan da aka yi wa wasu daga cikin iyalan Fasto Ezekiel Dachomo a jihar Filato
  • Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce dole ne a hukunta masu hannu a kisan tare da ƙara tsaurara matakan tsaro ga Kiristoci da sauran al'ummomin da ke cikin haɗari
  • Lamarin ya haifar da martani daga masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu suka nuna shakku kan matsayar gwamnatin Amurka kan matsalar tsaro a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin Amurka ta yi kakkausar suka kan kisan da aka yi wa wasu daga cikin iyalan Fasto Ezekiel Dachomo a jihar Filato, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici da matuƙar tayar da hankali.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta hannun sashen kula da harkokin Afirka ta bayyana hakan, inda ta ce hare-haren da ake kai wa Kiristoci da sauran al'ummomin da ke cikin haɗari a Najeriya na ƙara tayar da hankali.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: An yanke wa mutum 3 hukuncin daurin rai da rai kan sace daliban Oyo

Fasto Ezekiel Dachomo
Fasto Ezekiel Dachomo da Donald Trump. Hoto: Ezekiel Dachomo|Getty Images
Source: Twitter

Sanarwar da ta wallafa a Facebook ta kuma miƙa ta'aziyya ga iyalan mamatan da dukkan waɗanda wannan hari ya shafa.

Abin da Amurka ta ce

A cikin sanarwar, gwamnatin Amurka ta ce ta tattauna da jami'an gwamnatin Najeriya a makon da ya gabata kan yadda za a ƙarfafa matakan da za su hana irin waɗannan hare-hare sake faruwa.

Ta ce:

"Muna matuƙar yin Allah-wadai da mummunan kisan da aka yi wa wasu daga cikin iyalan Fasto Ezekiel Dachomo a jihar Filato."

Har ila yau, ta jaddada cewa wajibi ne a kamo tare da hukunta duk masu hannu a wannan kisan, tare da ɗaukar matakan gaggawa domin kare Kiristoci da sauran al'ummomin da ke cikin haɗari.

Sanarwar ta ƙara da cewa Amurka za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatin Najeriya wajen yaƙi da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi tare da tabbatar da cewa 'yan Najeriya suna gudanar da addininsu cikin 'yanci ba tare da tsoron hari ko muzgunawa ba.

Kara karanta wannan

Iran ta tayar da gobara a sansanin sojin Amurka bayan sakin bama bamai

Martanin jama'a kan sanarwar

Bayan wallafa sanarwar, mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu a kafafen sada zumunta.

Wani mai suna Jossymoore O. Ukaku ya ce:

"Yanzu na fahimci cewa Amurka ma ba ta da cikakken adalci. Jiya Trump ya yaba wa Tinubu, amma a wannan ranar aka kashe mutane a Zamfara."

Shi kuma Gonzuk Nenli ya ce:

"Fadar shugaban ƙasa ta ce Donald Trump ya yabawa gwamnatin Tinubu kan kare Kiristoci, bisa wata wasiƙa da aka ce an rubuta a ranar 6 ga Yuli."
Shugaba Donald Trump
Donald Trump na bayani a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A nasa bangaren, Okechukwu Ezugwu ya rubuta:

"Sai an gama shafe Kiristoci gaba ɗaya a Najeriya ne kafin Amurka ta ɗauki wani mataki?"

Shi kuwa Isaac Gber ya bayyana cewa:

"Muna fatan wannan Allah-wadai da Amurka ta yi ba zai tsaya nan ba kamar yadda aka saba gani a baya."

Trump ya yabawa Tinubu kan tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya yabawa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kan yadda yake jagorantar yaƙi da 'yan ta'adda a ƙasar.

Kara karanta wannan

'Yabon Trump ya nuna aikinmu ya na kyau': Fadar shugaban kasa

Trump ya bayyana a cikin wata wasiƙa cewa yana goyon bayan ƙoƙarin Tinubu na magance matsalolin tsaro, musamman hare-haren da ke shafar al'ummomin Kiristoci a Najeriya.

Haka kuma ya ce haɗin gwiwar Amurka da Najeriya na ci gaba da ƙarfafa wajen yaƙi da ta'addanci da sauran matsalolin tsaro da ke addabar wasu sassan ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng