Kano: Kotu Ta Sake Ba da Sabon Umarni Ga Likitoci Kan 'Yar Tiktok, Murja, Ta Fadi Dalili

Kano: Kotu Ta Sake Ba da Sabon Umarni Ga Likitoci Kan 'Yar Tiktok, Murja, Ta Fadi Dalili

  • Yayin da ake ci gaba da shari'ar 'yar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya a jihar Kano, Kotun Shari'ar Musulunci ta sake hukunci
  • Kotun da ke zamanta a Gama PRP a jihar Kano ta ba da umarnin duba lafiyar kwakwalwar matashiyar 'yar Tiktok din
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin matashiyar kan wasu zarge-zarge da suka hada da aikata badala da kuma yada karuwanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kotun Shari'ar Musulunci a Kano ta sake ba da sabon umarni kan shari'ar 'yar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya.

Kotun da ke zamanta a Gama PRP a jihar Kano ta umarci likitoci su duba lafiyar kwakwalwar Murja Kunya.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da shari'ar Murja Kunya

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar matashiyar 'yar Tiktok, Murja Ibrahim
Kotu ta umarci duba lafiyar kwakwalwar Murja Ibrahim. Hoto: Murja Kunya Ibrahim.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yi kan Murja?

Mai Shari’a Nura Yusuf Ahmad shi ya ba da umarnin a binciki lafiyar kwakwalwarta kan wasu zarge-zarge da ake yi akanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta kuma umarci a ajiye matashiyar 'yar Tiktok din karkashin kulawar likitoci da kuma hukumar Hisbah.

Alkalin ya bayyana cewa bisa ga dukkan alamu Murja ta nuna wani hali wanda yake nuna cewar kodai tana cikin maye ko kuma kwakwalwarta bata da lafiya.

A dalilin haka ne kotun ta ba da wannan umarni ga ma’aikatan lafiya su binkici kwakwalwarta don sanin abinda ke damunta, cewar Dala FM.

Cece-kuce kan sakin Murja daga gidan yari

Kotun ta kuma bayyana cewar Murja zata kwashe watanni uku a karkashin kulawar likitoci da hukumar Hisbah.

Lamarin shari’ar Murja ya dauki sabon salo ne bayan an gano cewa an sake ta daga gidan yarin Kurmawa, inda aka tsare da ita, sabanin umarnin kotun.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Shari'ar Musulunci ta yi hukunci kan 'yar Tiktok, Ramlat, ta fadi dalilai

Kakakin hukumar gidan yarin, Musbahu Lawan ya bayyana cewa kotun da ta ba da umarnin tsare Murja ce ta ba su umarnin sakinta a cikin wata takarda da aka kawo musu dauke da sa hannun alkalin, cewar Aminiya.

Kotu ta daure Ramlat 'yar Tiktok

A baya, mun ruwaito muku cewa Kotun Shari'ar Musulunci a jihar Kano ta yanke hukuncin dauri a gidan kaso ga ’yar Tiktok, Ramlat Muhammad.

Kotun ta yanke wa matashiyar ce hukuncin kan samun ta da laifin yada badala da kuma karuwanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel