Tinubu Ya Ware Minista 1 a cikin Mukarrabansa, Ya Koda Shi na Musamman
- Shugaba Bola Tinubu ya taya Ministan Ayyuka, David Umahi, murnar cika shekara 63, yana yabawa da jajircewarsa
- Tinubu ya bayyana Umahi a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ministocinsa masu ƙwazo, yana cewa kullum yana bibiyar ayyukan hanyoyi da gadoji a faɗin ƙasa
- Shugaban ya buƙaci Umahi ya ci gaba da hanzarta gina da gyaran hanyoyi domin inganta rayuwar 'yan Najeriya, tare da ƙarfafa ci gaban tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya taya Ministan Ayyuka, David Umahi, murnar cika shekara 63 da haihuwa.
Tinubu ya yaba da jajircewarsa wajen aiwatar da ayyukan more rayuwa masu ɗorewa a faɗin Najeriya.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga.
Kafin ya shiga majalisar ministocin gwamnatin Tinubu, Umahi wanda aka haifa ranar 25 ga Yuli, 1963, ya wakilci mazabar Ebonyi ta Kudu a Majalisar Dattawa.
Hakan ya biyo bayan kammala wa'adin mulki biyu a matsayin gwamnan Ebonyi daga 2015 zuwa 2023.
Tinubu ya bayyana Umahi a matsayin "ɗaya daga cikin fitattun ministocina masu ƙwazo."
Shugaban ya yabawa ministan saboda jajircewarsa wajen sauke nauyin aiki, yana mai cewa hankalinsa ya karkata wajen gina hanyoyi da gadoji masu ɗorewa da za su amfani 'yan Najeriya na tsawon shekaru masu yawa.
Sanarwar ta ce Tinubu ya yabawa Umahi kan ƙwazonsa, sadaukar da kai ga aiki, da kuma kishin ƙasa da yake nunawa wajen gudanar da ayyukansa.
Shugaban ya kuma buƙaci ministan ya ci gaba da wannan ƙwazo wajen gina sababbin hanyoyi, gyaran tsofaffi da kuma kammala ayyuka bisa manufar gwamnatinsa ta inganta rayuwar al'umma da bunƙasa tattalin arziki.
Tinubu ya ce Umahi ba ya zama kawai a ofishinsa ko dogaro da rahotannin ma'aikatansa, domin yana yawan zagaya wuraren ayyuka da kansa domin tabbatar da ana bin ƙa'idoji da amincewar da aka bayar.
A ƙarshe, shugaban ya yi wa Umahi da iyalansa fatan alheri, tare da yi masa addu'ar samun ƙoshin lafiya da ƙarin ƙarfi domin ci gaba da hidimtawa ƙasa.
Tinubu ya ce Umahi ba ya zama kawai a ofishinsa ko dogaro da rahotannin ma'aikatansa, domin yana yawan zagaya wuraren ayyuka da kansa domin tabbatar da ana bin ƙa'idoji da amincewar da aka bayar.
A ƙarshe, shugaban ya yi wa Umahi da iyalansa fatan alheri, tare da yi masa addu'ar samun ƙoshin lafiya da ƙarin ƙarfi domin ci gaba da hidimtawa ƙasa.
Umahi ya yaba Tinubu kan ayyuka a Arewa
A wani labarin, an ji cewa Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce kaso mafi tsoka na manyan ayyukan titunan gwamnatin Bola Tinubu suna Arewacin Najeriya.
Umahi ya bayyana cewa rabon ayyukan ya nuna gwamnati na kokarin tabbatar da ci gaba mai daidaito a fadin kasa na don kai.
Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya ce aikin babbar hanyar Gombe zuwa Biu zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da hada yankuna.
Asali: Legit.ng

