Shugaban INEC Ya Kwantar wa Yan Najeriya Hankali, Ya Yi Alkawari kan Zaben 2027

Shugaban INEC Ya Kwantar wa Yan Najeriya Hankali, Ya Yi Alkawari kan Zaben 2027

  • Yayin da ake shirin gudanar da zaben 2027, Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya yi alkawari ga 'yan Najeriya
  • Amupitan ya yaba wa Janar Abdulsalami Abubakar saboda gudunmawarsa wajen tabbatar da dimokuraɗiyya da zaman lafiya
  • INEC ta sanar da ranakun zaɓen 2027, tana roƙon 'yan Najeriya su ba hukumar cikakken goyon baya domin gudanar da sahihin zaɓe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya yi wa yan Najeriya alkawari.

Amupitan ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa za a yi amfani da kuma za a kidaya ƙuri'unsu a babban zaɓen shekarar 2027.

Alkwarin da shugaban INEC ya yi wa yan Najeriya kan zaben 2027
Shugaban hukumr INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, a gidansa da ke Minna a Jihar Niger, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Abin da Abdulsalami ya fadawa shugaban INEC game da APC, PDP, ADC gabanin 2027

Shugaban INEC ya yaba wa Abdulsalami Abubakar

Amupitan ya jagoranci tawaga mai kunshe da kwamishinonin ƙasa, sakataren hukumar, daraktoci da masu ba shi shawara kan harkokin fasaha zuwa wannan ziyara ta musamman.

Ya bayyana Abdulsalami Abubakar a matsayin uban dimokuraɗiyyar Najeriya, yana mai cewa miƙa mulki ga farar hula a shekarar 1999 ya kasance babban tarihi ga ƙasar.

Shugaban INEC ya ce hukumar tana kallon tsohon shugaban ƙasar a matsayin ginshiƙin goyon baya ga INEC da kuma jagora mai kishin dimokuraɗiyya.

Ya kuma yaba da rawar da Abdulsalami ke takawa a matsayin shugaban Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa, musamman wajen ƙarfafa yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin 'yan siyasa.

A cewarsa, wannan shiri ya ba masu ruwa da tsaki a siyasa damar yin alƙawarin guje wa tashin hankali tare da mutunta zaɓin al'ummar Najeriya.

INEC ta sha alwashin yin zaben gaskiya a 2027
Shugaban hukumar zabe ta kasa, INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Facebook

Shugaban INEC ya godewa Abdulsalami

Amupitan ya bayyana ziyarar a matsayin wata tafiyar nuna godiya saboda gudunmawar Abdulsalami wajen samar da zaman lafiya, gudanar da zaɓe cikin lumana da ƙarfafa dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

"Da an kai shi gidan yari"; Fadar shugaban kasa ta jikawa Atiku aiki kan taba Tinubu

Ya ce duk da matsin lambar da hukumar ke fuskanta, INEC za ta tabbatar cewa ra'ayin da 'yan Najeriya suka bayyana ta hanyar ƙuri'a shi ne zai yi nasara.

Shugaban hukumar ya ce manufarsa ita ce tabbatar da cewa talakawan Najeriya sun fita zaɓe cikin kwarin gwiwar cewa za a ƙidaya ƙuri'unsu yadda ya kamata.

Haka kuma, INEC ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya ranar 16 ga Janairun 2027, cewar Tribune.

Ta ƙara da cewa zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi kuma za su gudana ranar 6 ga Fabrairun 2027, yayin da Abdulsalami ya buƙaci 'yan Najeriya su mara wa INEC baya.

Sokoto ta ba da hutun karbar katin zabe

An ji cewa gwamnatin Ahmed Aliyu ta jihar Sokoto ta bayar da hutu ga jama'ar ta domin ba su dama su karbi katin zabensu gabanin kada kuri'a a 2027 mai zuwa.

An ɗauki matakin ne domin bai wa waɗanda ba su yi rajistar zaɓe ba damar samun katin PVC da zai ba su damar kada kuria'a don zabaen wanda su ke so.

Gwamna Ahmed Aliyu ya bukaci duknin 'yan jihar da su ka kai shekarun yin rajista da su tabbatar da cewa sun kammala kafin ranar 26 ga Yulin 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.