Inyamurai Sun Fadi Dalili 1 Da Yasa Ba Za Su Yi Zanga-Zangar Wahalar da Ake Sha a Mulkin Tinubu Ba

Inyamurai Sun Fadi Dalili 1 Da Yasa Ba Za Su Yi Zanga-Zangar Wahalar da Ake Sha a Mulkin Tinubu Ba

  • Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bayyana matsayinta yayin da zanga-zanga ke ci gaba da yaduwa a fadin kasar saboda matsin rayuwa da ake ciki
  • Shugaban kungiyar, Dr Emmanuel Iwuanyanwu, ya bayyana goyon bayansu ga Tinubu a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke kokawa kan manufofin gwamnati mai ci
  • A wata sanarwa daga sakataren kungiyar na kasa, Alex Ogbonna, Ohanaeze ta dage cewa Inyamurai ba za su shiga wannan tattaki ba saboda sun yarda Tinubu zai iya aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

A yayin da ake fama da matsin tattalin arziki a kasar, kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta sake yin alkawarin marawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.

Inyamurai sun ce ba za su shiga zanga-zangar tsadar rayuwa
Inyamurai Sun Fadi Dalili 1 Da Yasa Ba Za Su Yi Zanga-Zangar Wahalar da Ake Sha a Mulkin Tinubu Ba Hoto: Chief Dr. Emmanuel Iwuanyanwu CFR, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta sha alwashin kin yin zanga-zanga

Kungiyar ta sha alwashin yi wa Tinubu aiki a wannan mawuyacin hali da ake ciki, cewa shugaban kasar yana taimakawa 'yan Najeriya daga yankin kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

Farfesa ya bayyana kuskuren da Tinubu ya fara tafkawa kafin shiga Aso Villa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Dr Emmanuel Iwuanyanwu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar Alex Ogbonna, ya gabatarwa manema labarai, rahoton TVC.

Iwuanyanwu zai gana da masana tattalin arzikin Ndigbo

Iwuanyanwu ya tunatar da Ndigbo cewa basu da wata matsala ta kashin kai da shugaban kasar, sannan ya bukaci ‘yan kasar da kada su bari a yi amfani da su wajen gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin tarayya, rahoton Punch.

Ya koka cewa Inyamurai na fuskantar matsaloli da dama ciki harda nunawa mutanen Kudu maso Gabas wariya: wajen nade-naden mukamai a gwamnatin baya.

Ya kuma nuna fatan cewa gwamnatin Tinubu za ta gyara wadannan kura-kuran nan da 'dan lokaci.

Sai dai kuma, Iwuanyanwu ya yi alkawarin kiran taro na manyan masana tattalin arziki na Inyamurai domin samar da dabarun shawo kan matsalolin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnonin PDP sun nemi Tinubu ya yi murabus, sun fadi dalili

Yaron Tinubu ya nemi a kara hakuri

A wani labarin, Folashade Tinubu-Ojo wanda diya ce a wajen Mai girma Bola Ahmed Tinubu ta yi kira ga mutane su kara hakuri da gwamnati.

Folashade Tinubu-Ojo kamar yadda The Cable ta rahoto, tayi wannan kira ne a wajen maulidin da Aljamahatul Qadiriyyah suka shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel