Ana Maganar Rashin Lafiya bayan Kwana 48 Paul Biya bai Koma Kamaru ba
- Rashin kasancewar shugaban kasar Kamaru, Paul Biya, a gida har na tsawon kwanaki 48 ya jawo mahawara kan rashin tasirin ayyukan gwamnatin kasar
- Jam'iyyun adawa na korafin cewa an samu babban gurbin shugabanci a kasar sakamakon jinkirin dawowar shugaban mai shekaru 93 daga Switzerland
- Sai dai makusanta da jami'an gwamnatin kasar sun musanta zargin, inda suka jaddada cewa shugaban yana gudanar da ayyukansa kamar yadda ya kamata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Cameroon – Rashin ganin shugaban kasar Kamaru, Paul Biya, wanda yake kasar Switzerland tun farkon watan Yunin 2026, ya sake rura wutar mahawara kan jinkirin ayyukan gwamnati a kasar da al'umma ke da bukatar sauyi.
A yau Asabar an cika kwanaki 48 rabon da Biya, mai shekaru 93, wanda ya shafe sama da shekaru 40 a kan karagarsa kuma shi ne shugaban kasa mafi tsufa a duniya, da ya bar kasar Kamaru.

Source: Facebook
RFI ta rahoto cewa wata sanarwa a hukumance ta bayyana cewa ya bar kasar ne tun ranar 7 ga watan Yunin 2026 domin gudanar da "gajeren hutu a Turai" tare da matarsa Chantal Biya.
Martanin gwamnatin Kamaru
Shugaban, wanda ya sha gudanar da tsalle-tsalle akai-akai zuwa Geneva a tsawon shekarun da suka gabata, ya fuskanci jita-jita da rade-radi mabambanta game da lafiyarsa, wadanda a wani lokacin gwamnati ke musantawa.
Sakamakon rahotannin da aka wallafa a jaridu, Ministan Watsa Labarai Rene Emmanuel Sadi ya fitar da sanarwa a ranar 18 ga watan Yuni, inda ya musanta cewa ana jinyar Biya a wani asibiti da ke Geneva.
Sannan mataimakin shugaban jam’iyyar MRC, Mamadou Mota, ya bayyana a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a cewa rashin ganin Biya yana nuna "babban gurbin shugabanci a cibiyoyin gwamnati".
Korafin 'yan kasar Kamaru
A gefe guda, Reuters ta wallafa cewa jam’iyyar adawa ta SDF a ranar Juma’a ta ce kasar tana tafiya ne kamar motar da babu direba.
Haka zalika, masanin kimiyyar siyasa Stephane Akoa ya bayyana cewa:
"Ana ci gaba da samun rahotannin da ke nuna rikicin cikin gida tsakanin bangarori daban-daban tsakanin makusantansa."
Akoa ya kara da cewa daya daga cikin bangarorin da ke taka rawa sosai shi ne bangaren uwargidan shugaban kasa, Chantal Biya.
Ya bayyana ta a matsayin wacce ke kara kasancewa sosai a cikin huldar gwamnati tare da ambaton sunanta akai-akai wajen yanke shawarwari da gudanar da nade-nade.

Source: Getty Images
Tinubu zai je Saudiyya
A wani labarin daban, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu, a ranar Juma'a, ya karbi gayyata daga Yariman mai jiran gado Mohammed bin Salman bin Abdulaziz.
Jakadan Saudi Arabia a Najeriya, Yousef Albalawi ne ya mika gayyatar a ranar Juma'a yayin wata ziyara da ya kai wa Shugaban a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Sakon ya bayyana cewa Albalawi ya mika gayyatar ne a madadin yariman mai jiran gado na Saudi Arabiya, inda ya gayyaci Shugaba Tinubu domin halartar taron masu zuba jari a kasar.
Asali: Legit.ng

