Gwamnati Ta Bankado Hanyoyi 32 Na Safarar Abinci Daga Najeriya Zuwa Kasashen Waje

Gwamnati Ta Bankado Hanyoyi 32 Na Safarar Abinci Daga Najeriya Zuwa Kasashen Waje

  • Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta gano wasu barayin hanyoyi 32 da ake amfani da su wajen fasa kwabrin kayan abinci
  • Kashim Shettima ya bayyana hakan a wajen wani taro kan harkokin kula da dukiyar al’umma da aka gudanar a Abuja
  • Shettima ya ce daga lokacin da aka gano hanyoyin, an kama motoci 45 dauke da masara ana shirin fitar da su zuwa wasu kashahe

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce ta gano hanyoyi 32 da ake safarar kayan abinci daga Najeriya zuwa wasu kasashen ba bisa ka'ida ba.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana hakan a ranar Talata a wajen wani taro kan harkokin kula da dukiyar al’umma da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kano da sauran jihohi 3 da aka gudanar da mummunar zanga-zanga a Najeriya

Shettima ya ce barayin hanyoyin 32 suna a yankin Ilela.
Shettima ya ce barayin hanyoyin 32 suna a yankin Ilela. Hoto: @officialSKSM
Asali: Facebook

Ya ce a tsakar daren Lahadi ne aka kama manyan motoci 45 da ke dauke da masara yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kasashe makwabta, rahoton Voice of Nigeria.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama motoci 45 dauke da masara za a kai waje

Mataimakin shugaban kasar ya ce:

“Kwanaki uku da suka wuce, an kama manyan motoci 45 dauke da masara ana jigilar su zuwa kasashen makwabta. A yankin Ilela kawa, akwai hanyoyin fasa kwabri guda 32.
"Jum kadan bayan da aka kama wadannan kayan abincin, farashin masara ya fadi da N10,000. Yanzu buhu ya koma naira dubu 50 daga naira dubu 60."

Wasu 'yan siyar na yi wa gwamnati zagon kasa - Shettima

Shettima, wanda ya yarda cewa Najeriya ta shiga cikin mawuyacin hali, ya kuma tabbatar wa al’ummar kasar cewa ba za a dauwama a yanayin ba na har abada, Chanels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kashe kasurgumin dan bindiga a Arewa, sun kwato muggan makamai

Sai dai ya yi Allah wadai da yadda ya ce wasu na rura wutar rarrabuwar kawuna da tashin hankali saboda halin da ake ciki a kasar.

“Akwai wadanda ke da niyyar jefa kasar nan cikin wani hali na rashin zaman lafiya. Wadanda suka gaza samun mulki ta hanyar zabe, yanzu suke yi wa gwamnati makarkashiya."

- A cewar Shettima.

Hukumar ZARTO ta tare motocin abinci da ke shirin shiga Nijar

Tun da farko, Legit Hausa ta ruwaito yadda jami'an hukumar sufuri ta jihar Zamfara (ZARTO) ta tare wasu motoci 45 da ke shirin shiga jamhuriyyar Nijar dauke da masara.

Wannan ya biyo bayan umarnin shugaban kasa na karfafa tsaro don dakile boye kayan abinci ko safararsu ba bisa ka'ida.

Kakakin hukumar ZARTO, Sale Shinkafi ya ce sun kama motocin suna kokarin bi ta wasu barayin hanyoyi don shigar da kayan Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel