'Tun Gwamnatin Buhari ne': An Gano Lokacin da Hukumar Bogi Ta PFIPC Ta Kafu
- Ofishin Kasafin Kudi a Najeriya ya binciko adadin shekaru da hukumar bogi ta PFIPC ta yi a kasar
- Ya ce PFIPC ba ta samo asali a gwamnatin Shugaban kasa, Bola Tinubu ba kamar yadda wasu suke tunani
- Darakta Janar na hukumar, Tanimu Yakubu ya bayyana cewa an ware wa PFIPC kudi ne bayan hukumomi sun ba ta lamba da izinin aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ana ci gaba da samun sababbin bayanai game da Hukumar bogi ta PFIPC da aka kirkira a Najeriya.
PFIPC da fadar shugaban kasa ta bayyana cewa hukumar samo asali ne daga Majalisar Tattalin Arziki a mulkin marigayi Muhammadu Buhari.

Source: Twitter
Hakan na kunshe cikin bayanin Ofishin Kasafin Kudi bayan zaman majalisar wakilai, cewar Vanguard.
Yadda PFIPC ta shiga cikin kasafin kudi
Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kudi, Tanimu Yakubu, ya ce ba PFIPC ce ta tilasta a saka ta cikin kasafin kudin 2026 ba.
Ya bayyana cewa hukumomin gwamnati sun riga sun fitar da takardun da suka ba ta lambar gudanarwa da wasu amincewa.
A cewarsa, Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya bai wa PFIPC lambar gudanarwa, yayin da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Tarayya ya amince da tsarin ma’aikata da izinin daukar aiki.
Yakubu ya kara da cewa aikin Ofishinsa shi ne tantance tasirin kudaden da ake bukata bisa takardun da suka samu daga hukumomin da ke da alhakin bayar da irin wadannan amincewa.
Ya bayyana cewa PFIPC ta nemi a ware mata N3.85 biliyan domin albashin ma’aikata a kasafin kudin 2026.
Bayan amfani da tsarin ma’aikata da ka’idojin albashi na gwamnati, Ofishin Kasafin Kudi ya rage adadin zuwa N802.978 miliyan.
Ya jaddada cewa wannan adadi ba kyauta ba ce ga PFIPC, domin Ofishin Kasafin Kudi ne ya yi lissafinsa bisa ka’idojin gwamnati da tsarin kididdigar kudade.
Yakubu ya ce hukumar PFIPC ba ta samu izinin karshe na Financial Clearance ba, wanda ke tabbatar da cika sharuddan daukar ma’aikata da fara kashe kudin albashi.

Source: Facebook
Yadda ya kamata a biya ma'aikatar PFIPC
A cewarsa, ko da a tsarin doka ma, ba za a bai wa hukumar duk kudin albashi gaba daya ba, ya ce ana biyan ma’aikata ne kowane wata kai tsaye ta asusun bankin ma’aikatar, kamar yadda Punch ta ce.
Yakubu ya ce babu ko sisi da aka cire daga kudin albashin da aka ware wa PFIPC, saboda ba a taba fara tsarin daukar ma’aikata ko biyan albashi ba.
Rigimar PFIPC ta fito fili ne bayan Femi Gbajabiamila ya bayyana ta a matsayin hukumar bogi tare da kai korafi ga jami’an tsaro a watan Yunin 2026.
Sai dai shugaban PFIPC, Prince Adeniyi Adeyemi, ya musanta ikirarin fadar shugaban kasa tare da zargin Gbajabiamila da neman kudade domin tabbatar da nadinsa, zargin da ya musanta tare da kai karar bata suna.
Adeyemi ya tsorata da badakalar PFIPC
An ji cewa Adeniyi Adeyemi da ke ikirarin shugabantar PFIPC ya ce dalilin da ya sa ya daina fitowa fili shi ne barazanar da ake yi wa rayuwarsa.
Ya sake jaddada zargin cewa ya biya Naira miliyan 400 domin samun mukamin shugaban hukumar PFIPC.
Fadar shugaban kasa ta dage cewa PFIPC ba a san da zamanta ba, yayin da Shugaba Tinubu ya ba da umarnin gudanar da bincike.
Asali: Legit.ng


