Rayuka da Dama Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota

Rayuka da Dama Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota

  • An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a kan titin hanyar Legas zuwa Abeokuta a ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu
  • Hatsarin motan wanda ya ritsa da mutum 17 ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum tara yayin da wasu mutum bakwai suka jikkata
  • Kakakin hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ogun, ta ce hatsarin ya auku ne sakamakon gudu wanda ya wuce ƙima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Mutum tara ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a garin Kere da ke ƙaramar hukumar Ewekoro a jihar Ogun.

Mummunan hatsarin wanda ya afku a ranar Talata a kan hanyar Legas zuwa Abeokuta, ya kuma jawo wasu mutum bakwai sun jikkata, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan mutane da dama sun rasu a wani mummunan hatsarin mota

An samu hatsarin mota a titin Legas-Abeokuta
Hatsarin motan ya ritsa da mutum 17 Hoto: @FRSCNigeria
Asali: Twitter

Jaridar Nigerian Tribune ta ce kakakin hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar hatsarin a wata sanarwa da ta fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamanta:

"Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 a kan hanyar Legas zuwa Abeokuta. Kimanin mutum 17 ne hatsarin ya ritsa da su, mutum bakwai sun jikkata, sannan mutum tara suka rasa ransu."

Menene ya haddasa hatsarin motan?

A cewar kakakin, abubuwan da ake zargin sun haddasa hatsarin sun haɗa da gudun wuce gona da iri da kuma keta dokar tuƙi wanda ya yi sanadiyyar motoci biyu suka yi taho mu gama.

Kakakin ta ci gaba da cewa:

"An kai waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Ijaye yayin da aka ajiye gawarwakin a asibitin Lantoro da babban asibitin Ijaye Abeokuta."

Kara karanta wannan

Bayin Allah da yawa sun mutu yayin da ƴan bindiga suka buɗe wa jama'a wuta a jihar Arewa

Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar, Anthony Uga ya gargaɗi masu ababen hawa kan saɓa dokar tuƙi da gudun da ya wuce ƙima, yana mai nuni da illolin dake tattare da laifukan guda biyu.

Ya kuma shawarci masu ababen hawa da su bi ka’idojin zirga-zirga da kuma jajantawa iyalan waɗanda hadarin ya ritsa da su.

Hatsarin Mota Ya Salwantar da Rayuka a Ondo

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani mummunan hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Ore cikin ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo ya salwantar da rayukan mutum 10.

Hukumomi sun bayyana cewa hatsarin motan ya auku ne bayan wata motar safa ɗauke da fasinjoji ta yi ƙundumbala cikin wani rami.

Asali: Legit.ng

Online view pixel