Amurka Ta Gano Hatsarin da Mojtaba Khamenei Ke da Shi fiye da Mahaifinsa kan Nukiliya

Amurka Ta Gano Hatsarin da Mojtaba Khamenei Ke da Shi fiye da Mahaifinsa kan Nukiliya

Hasken Labarai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Rahotannin leken asirin Amurka sun ce gano wasu sababbin bayanai ga/me da sabon jagoran Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei
  • Jami'an Amurka sun ce Mojtaba Khamenei ya ji munanan raunuka a yakin, amma har yanzu yana jagorantar gwamnati
  • Iran ta kwashe wasu na'urorin tace uranium zuwa tsibirin Pickaxe domin kare su daga hare-haren Amurka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Hukumomin leken asirin Amurka sun samu wasu bayanan sirri kan sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei.

Hukumomin sun yi imanin cewa Mojtaba ya fi mahaifinsa da wanda ya gada sha'awar mallakar makamin nukiliya.

Amurka ta gano wani lamari game da Mojtaba Khamenei
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Alkawarin marigayi kan makamin nukiliya

Mahifinsa Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe a farkon yakin cikin harin Isra'ila da bayanan sirrin Amurka suka taimaka, ya yi alkawarin ba zai kera makamin nukiliya ba, cewar New York Times.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗaure wani mutumi a gidan kaso bayan kisan ƴar majalisa da mijinta

Duk da cewa jami'an Amurka sun dade suna zargin Iran da son mallakar makamin nukiliya, mutane da dama sun yi imanin cewa Ali Khamenei yana da gaskiya wajen kin hakan.

Sabon jagoran bai taba yin kira a bainar jama'a da a gina makamin nukiliya ba, Sai dai hukumomin leken asirin Amurka na ganin yana da irin wannan buri.

Sun kuma yi imanin cewa sabuwar gwamnatin masu tsattsauran ra'ayi da ta fito bayan kashe shugabannin Iran da dama tana son bunkasa manyan makaman nukiliya.

Gwamnatin Iran ta kara kokarin tabbatar da iko kan mashigar Hormuz, sannan ta kasance mai wahalar tattaunawa da kasashen yamma kan muhimman batutuwa.

Idan yakin Amurka da Isra'ila ya sa Tehran ta kara sha'awar mallakar makamin nukiliya, hakan zai zama wani babban sakamako na kashe tsohon jagoran kasar.

Amurka na zargin Mojtaba da tsananin ra'ayi kan makamin nukiliya
Sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Gargadin da jami'an Amurka suka yi

Jami'an Amurka sun yi gargadin cewa yawancin bayanan leken asiri kan Mojtaba Khamenei sun samo asali ne kafin barkewar wannan yaki.

Sun ce ya samu munanan raunuka a farkon yakin, kuma ya rage bayyana a fili da sadarwa saboda raunukan da kuma tsoron harin sama.

Kara karanta wannan

Kasar Isra'ila ta kai hare hare Gaza, ta kashe Falasdinawa

A cewar jami'an, Mojtaba Khamenei har yanzu shi ke jagorantar gwamnatin Iran, amma ba shi da cikakken iko da tasirin da mahaifinsa ya mallaka tsawon shekaru 36.

Wannan rahoto na fitowa ne yayin da Shugaba Donald Trump ke nazarin yiwuwar kara tsaurara hare-haren soji kan Iran, cewar Times of Israel.

Jami'an Amurka sun ce Tehran ba ta sake farfado da shirinta na nukiliya ba, amma ta dauki matakan kare kadarorinta bayan hare-haren bara.

Rahotanni sun ce Iran ta kwashe wasu na'urorin tace uranium zuwa wani katafaren rami mai kariya da ake kira tsibirin Pickaxe a tsakiyar kasar.

Jami'an Amurka sun ce wannan mataki na iya zama farkon sake gina karfin tace uranium, amma a yanzu Iran na kokarin kare kayanta daga hare-haren bama-baman Amurka.

Gargadin Mojtaba Khamenei ga Trump

A baya, an ji cewa yayin da sabon rikici ke son barkewa, Mojtaba Khamenei ya ce kasashen Gabas ta Tsakiya ba za su sake zama mafaka ga sansanonin sojin Amurka ba.

Tun bayan hawansa matsayin jagoran addini mafi girma na Iran, Mojtaba bai taba fitowa a bidiyo ko a gaban kyamara ba amma ya sha tura sakon gargadi.

A daya bangaren kuma, rundunar IRGC ta Iran ta ce ta harbo jirgin MQ-9 Reaper na Amurka, ta kuma harbi F-35 da jirgin leken asiri a sararin samaniyarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.