'Yan Bindiga Sun Sace Babban Dan Siyasa, Matarsa da 'Ya'yansa a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Sace Babban Dan Siyasa, Matarsa da 'Ya'yansa a Zamfara

  • Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari gidan shugaban ƙaramar hukumar Bungudu a Zamfara tare da yin garkuwa da shi da wasu daga cikin iyalansa
  • Maharan sun kashe jami'an tsaro huɗu da suka haɗa da 'yan sanda biyu da masu sintiri biyu kafin su tsere da shugaban ƙaramar hukumar
  • Rahotanni sun ce jami'an tsaro sun ceto wasu daga cikin 'ya'yan shugaban ƙaramar hukumar yayin da ake bibiyar maharan, amma an tafi da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara – Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara, Alhaji Nura Umar Bungudu, bayan kai wani mummunan hari a gidansa.

An ce maharan sun kutsa cikin garin Bungudu ne a daren ranar Alhamis, inda suka nufi gidan shugaban ƙaramar hukumar da ke unguwar Zango, mai tazarar kasa da kilomita 20 daga babban birnin jihar, Gusau.

Kara karanta wannan

Kasar Isra'ila ta kai hare hare Gaza, ta kashe Falasdinawa

Nura Umar Bungudu
Shugaban karamar hukumar da aka sace, Nura Umar Bungudu. Hoto: Mashkur Yahaya Bug
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa jami'an tsaron da ke gadin gidan sun yi ƙoƙarin dakile harin, amma maharan sun fi su ƙarfin makamai.

Yadda aka sace dan siyasar

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe 'yan sanda biyu da masu sintiri biyu kafin su yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar.

Ya ce ɗaya daga cikin masu sintirin da aka kashe ya kasance yana taka muhimmiyar rawa wajen kare garin daga hare-haren 'yan bindiga.

A cewarsa, maharan sun zo da makamai masu ƙarfi da kuma adadi mai yawa, abin da ya sa jami'an tsaron suka kasa dakile harin duk da juriyar da suka nuna.

An ceto wasu daga cikin 'ya'yansa

Majiyar ta ce tun farko 'yan bindigar sun yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar tare da matarsa da 'ya'yansu.

Sai dai bayan jami'an tsaro sun bi sawun maharan, sun yi nasarar ceto yara huɗu ko biyar daga cikin waɗanda aka sace.

Kara karanta wannan

Ba adalci: Kanawa sun yi martani da Gwamna ya raba filaye, N100m ga yan dangwale

Duk da haka, shugaban ƙaramar hukumar ya ci gaba da kasancewa a hannun maharan bayan sun tsere da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

DCL Hausa ta wallafa a Facebook cewa ƙarin jami'an tsaro sun isa wurin ne bayan maharan sun riga sun kammala aikinsu kuma sun tsere.

Taswirar jihar Zamfara
Taswirar jihar Zamfara a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba, domin ƙoƙarin samun kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, bai yi nasara ba.

Sokoto ta ƙarfafa tsarin tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Sokoto ta yaye jami'an Sokoto Marshals (SOSMA) 1,550 domin ƙarfafa tsaro a faɗin jihar.

Jami'an sun haɗa da masu kula da tsaro, zirga-zirga, tattara bayanan sirri da kuma kare kadarorin gwamnati, ciki har da mata 70 da aka ɗauka a karon farko.

Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, wanda ya halarci bikin, ya yabawa gwamnatin Sokoto bisa wannan mataki, yana mai cewa abin koyi ne wajen ƙarfafa tsarin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng