Da Gaske Ndume Ya Taba Karbar Kudin Fansa ga Boko Haram? Gaskiya Ta Fito

Da Gaske Ndume Ya Taba Karbar Kudin Fansa ga Boko Haram? Gaskiya Ta Fito

  • Sanata Ali Ndume ya yi martani game alakanta shi da ake yi da Boko Haram musamman a kwanakin nan
  • Ndume ya musanta zargin cewa ya karɓi kuɗin fansa ko ya shiga sulhu tsakanin gwamnati da Boko Haram, yana cewa tun farko yana adawa da hakan
  • Sanatan ya ce bai taɓa goyon bayan biyan kuɗin fansa ko tattaunawa da Boko Haram ba, yana mai cewa wannan matsayinsa ne tun a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Ana ci gaba da maganganu kan alakanta Sanata Ali Ndume da Boko Haram a yan kwanakin nan.

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya musanta zargin cewa ya taɓa karɓar kuɗin fansa ko zama mai shiga tsakani tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar Boko Haram.

Kara karanta wannan

Yadda wani dan majalisar wakilan Najeriya ya gagara biyan kudin makarantar 'yarsa

Ndume ya ƙaryata alaka da Boko Haram
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno a Najeriya. Hoto: Mohammed Ali Ndume.
Source: Facebook

Da yake magana a shirin Politics Today na Channels Television, Ndume ya ce bai taɓa goyon bayan tattaunawa da Boko Haram ko biyan kuɗin fansa ba.

Martanin da Ndume ya yi ga Kaigama

Ndume ya mayar da martani ne ga zargin shugaban ƙungiyar Borno South Youth Alliance, Samaila Kaigama, wanda ya ce sanatan ya shiga tattaunawar sakin mutanen Ngoshe da aka sace.

Kaigama ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta bai wa Ndume Naira biliyan biyar domin tattaunawa da Boko Haram, amma biliyan 1.9 kacal aka bai wa ƙungiyar.

Ya bayyana cewa tun farko yake adawa da irin wannan mataki, har ma a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari lokacin da aka yi musayar fursunoni da wasu tattaunawa.

Ndume ya ce ba zai iya magana a madadin gwamnati ba, amma ya bayyana cewa wasu da suka yi ikirarin zama masu shiga tsakani sun kasance masu damfara.

Ya ce wasu daga cikin waɗannan mutane an daure su, wasu kuma suna tsare ko kuma ana ci gaba da bincikensu saboda zargin yaudara.

Kara karanta wannan

An bayyana yadda Yariman Saudiyya Abdullah bin Fahad ya rasu a otal din Landan

Sanatan ya ce gwamnatin tarayya na gudanar da bincike kan zargin Kaigama, wanda ya ce gwamnati ta ba shi Naira biliyan biyar domin sulhu da Boko Haram.

Ana zargin Ndume da alaka da Boko Haram
Sanatan Borno ta Kudu a Najeriya, Ali Ndume. Hoto: Senator Mohammed Ali Ndume.
Source: Twitter

Boko Haram: Ndume ya kalubalanci Kaigama

Ndume ya tambayi wanda ya naɗa Kaigama a matsayin mai shiga tsakani tsakanin kansa da Boko Haram, yana mai nuna shakku kan ikirarinsa.

Sanatan ya kuma tuna cewa a shekarar 2011 an tsare shi na kusan wata ɗaya da rabi bisa zargin alaƙa da wani da ake kira mai shiga tsakanin Boko Haram.

Ya ce bayan shari'ar da ta ɗauki shekaru shida, kotu ta wanke shi saboda babu wata hujja da ta tabbatar da zargin da aka yi masa.

A ƙarshe, Ndume ya ce mafi dacewa shi ne a gayyaci Kaigama domin ya gabatar da hujjojin da ke goyon bayan zarge-zargen da ya yi.

Ndume ya magantu bayan ganawa da Tinubu

An ji cewa Sanata Ali Ndume ya bukaci shugaba Tinubu da ya daina tura hadimansa su yi jawabi a madadin sa, ya fito kai tsaye ya yi magana da jama'a.

Ndume da ya ziyarci Aso Rock ya tattauna da Tinubu kan rashin tsaro, tsadar kayayyaki da halin da jama'ar Arewa maso gabas ke ciki.

Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin duba korafin, haka kuma ya nemi a rika gudanar da irin wannan tattaunawa da Sanata Ndume akai-akai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.