Tinubu Ya Firgita da Atiku Ya Ce zai Maido Tallafin Mai, Ya Yi Martani Mai Zafi

Tinubu Ya Firgita da Atiku Ya Ce zai Maido Tallafin Mai, Ya Yi Martani Mai Zafi

  • Shugaba Bola Tinubu ya ce alƙawarin Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur idan ya ci zabe ya nuna rashin fahimtar yadda gwamnati ke aiki
  • Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan alƙawarin da ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC ya yi na dawo da tallafin man fetur
  • Shugaban ƙasar ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya karɓi Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, wanda ya kai masa ziyara bayan cin zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya caccaki alƙawarin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a 2027.

Tinubu ya ce irin wannan alƙawari ya nuna rashin fahimtar yadda harkokin gwamnati da tattalin arzikin Najeriya ke gudana, yana mai cewa cire tallafin ya taimaka wajen sauya yanayin kuɗin jihohi.

Kara karanta wannan

Atiku ta tayar wa Tinubu hankali kan kudirin dawo da tallafi idan ya yi nasara

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Paul O. Ibe|Bayo Onanuga
Source: Facebook

The Cable ta rahoto cewa Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis lokacin da ya karɓi Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun a fadar shugaban ƙasa.

Tinubu ya soki alƙawarin Atiku

Shugaba Tinubu ya ce ya ji labarin yadda ɗaya daga cikin masu hamayyarsa ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A cewarsa, wannan magana ta nuna rashin fahimta sosai kan shugabanci da kuma yanayin tattalin arzikin ƙasar.

Daily Trust ta wallafa cewa ya ce:

"Na ga ɗaya daga cikin masu hamayya da ni ya ce zai dawo da tallafi. Na karanta maganar. Wannan wata alama ce ta rashin fahimta sosai game da shugabanci da tattalin arziki.
"Kafin na zo nan, jihohi 27 ba su iya biyan albashi, balle kuma a yi maganar fansho. Ana bin ma'aikata albashi, yayin da gwamnatocin jihohi suka dogara kacokam kan gwamnatin tarayya."

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: An gano bashi ya yi wa Amurka katutu yayin da ta ke yaki da Iran

Tinubu ya ba Adeleke shawara

A yayin ziyarar, Tinubu ya shawarci Gwamna Ademola Adeleke da ya yi amfani da nasararsa wajen haɗa kan al'ummar jihar Osun tare da kauce wa muzgunawa ko nuna wariya ga abokan hamayyarsa.

Ya ce nasara a zaɓe ba ta nufin an ci yaƙi ko an mallaki masu hamayya, illa dai damar ce ta yin aiki domin inganta rayuwar al'umma.

Gwamna Ademola Adeleke
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke. Hoto: Osun State Government
Source: Facebook

Tinubu ya kuma ce ya kamata Adeleke ya mayar da hankali kan samar da abubuwan more rayuwa, gyaran makarantu da asibitoci, inganta harkar lafiya da kuma kare marasa ƙarfi a cikin al'umma.

Atiku zai maido tallafin mai

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban Najeriya a babban zaɓen 2027.

Atiku ya ce gwamnatin tarayya ta gaza bayyana yadda aka yi amfani da kuɗin da aka ce an samu bayan cire tallafin, yana mai cewa duk wanda aka samu da satar kuɗin za a tilasta masa mayar da su.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta bayyana cewa cire tallafin man fetur da sauye-sauyen da aka yi a tsarin tattalin arziki sun samar da Naira tiriliyan 15.8.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng