Magana Ta Girma: Atiku na Neman Bahasi daga Tinubu kan Kudaden Cire Tallafi
- Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya ta bayyana wa ’yan Najeriya yadda ta kashe kudaden da ta tara bayan cire tallafin man fetur
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce cire tallafin ya jefa ’yan Najeriya cikin tsadar man fetur, sufuri da abinci, tare da rage karfin sayayya
- Atiku ya kalubalanci gwamnatin Tinubu da ta bincike shi idan tana da hujjar almundahana, yana mai cewa farfaganda ba za ta maye gurbin shaida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya kalubalanci gwamnatin tarayya kan kudaden cire tallafi.
Atiku ya bukaci gwamnatin da ta yi wa ’yan Najeriya bayani kan yadda aka kashe kudaden da aka samu bayan cire tallafin man fetur.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, babban mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai, ya fitar, cewar TheCable.
Cire tallafi: Kalubalen Atiku ga gwamnatin Bola Tinubu
Atiku wanda ke takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da magoya bayanta na kokarin karkatar da hankalin jama’a daga tambayoyin da ake yi kan yadda ake tafiyar da dukiyar kasa.
Atiku ya ce gwamnati ta cire tallafin man fetur tare da bukatar ’yan Najeriya su jure wahalhalun da hakan ya haifar, bisa alkawarin cewa za a mayar da kudaden da aka samu wajen ayyukan ci gaba.
Ya ce:
“Sun cire tallafin daga hannun talakawa, suka yi alkawarin cewa wannan sadaukarwar za ta samar da kudaden gudanar da ayyukan ci gaba. ’Yan Najeriya sun amince su sha wahala matuka saboda wannan alkawari."

Source: Twitter
Atiku ya koka kan tsadar abinci, sufuri
Atiku ya ce farashin man fetur, sufuri da abinci ya karu, yayin da karfin sayen kayayyaki na ma’aikatan Najeriya ya ragu matuka, cewar Daily Post.
Ya kara da cewa:
“A yau, man fetur ya kara tsada, sufuri ya kara tsada, abinci ya kara tsada, sannan karfin sayen kayayyaki na ma’aikacin Najeriya ya lalace sosai.”
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma tambayi dalilin da ya sa gwamnati ke ci gaba da bayar da tallafin haraji, rangwamen haraji, kudaden biyan haraji da wasu gata ga manyan ’yan kasuwa da ya bayyana a matsayin masu karfin tattalin arziki
Ya ce gwamnati ba za ta iya cire tallafin da ke taimaka wa talakawa ba, ta amfana da karin kudaden shiga, sannan ta rika bayyana shirye-shiryen rage wahala a matsayin abubuwan da ba su dace da tattalin arziki ba.
“Saboda haka, tambayarmu har yanzu mai sauki ce: ina kudin al’umma suke?”
Atiku ya dura kan azzalumai a Najeriya
Mun ba ku labarin cewa Atiku Abubakar da ke takarar shugaban kasa a inuwar ADC ya zargi masu mulki da satar zabe da kuma lalata tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan
An gano manyan hadurra 3 a shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ga 'yan Najeriya
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya sake tabbatar da cewa zai dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi a 2027.
Atiku ya ce cire tallafin man fetur ya jefa karin ‘yan Najeriya cikin talauci, yayin da Tinubu ya soki manufarsa da cewa akwai yaudara a ciki.
Asali: Legit.ng

