Bankuna da Wurare 32 da za a iya Sayen Hannun Jarin Matatar Dangote

Bankuna da Wurare 32 da za a iya Sayen Hannun Jarin Matatar Dangote

  • Matatar Dangote ta amince da bankuna, kamfanonin fasahar kuɗi da sauran dandaloli 32 da masu zuba jari za su yi amfani da su wajen sayar da hannun jari
  • Kamfanin ya wallafa jerin sunayen hanyoyin a shafinsa na IPO, inda ya gargadi masu zuba jari da su yi amfani da hanyoyin da aka amince da su kawai
  • Rahotanni sun bayyana cewa hanyoyin sun ƙunshi bankuna 19, kamfanonin fasahar kuɗi 10, kamfanonin sadarwa biyu da NGX Invest

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Bankunan da aka amince da su

Abuja – Matatar Dangote ta fitar da cikakken jerin bankuna da sauran wuraren da masu zuba jari za su iya amfani da su wajen sayen hannun jarin matatar.

A cewar kamfanin, masu zuba jari ya kamata su yi rajista ta hanyoyin da aka tabbatar da su kawa domin kaucewa fadawa tarkon 'yan damfara.

Kara karanta wannan

Asiri ya fara tonuwa: An kama mutum 2 kan kashe Danshagamu a Kano

Alhaji Aliko Dangote
Aliko Dangote a hagu da matatar shi a dama. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Punch ta wallafa jerin wuraren da matatar Dangote ta amince da su a matsayin sahihan hanyoyin sayen hannun jari.

Ga bankuna 19 da aka amince da su:

  1. Bankin Access
  2. Bankin Eco
  3. FCMB
  4. Bankin Fidelity
  5. First Bank
  6. Bankin Globus
  7. GTCO
  8. Bankin Jaiz
  9. Bankin Keystone
  10. Bankin Lotus
  11. Bankin PremiumTrust
  12. Bankin Providus
  13. Stanbic IBTC
  14. Bankin Sterling
  15. TAJ Bank
  16. UBA
  17. Union Bank
  18. Bankin Wema
  19. Bankin Zenith

Kamfanonin fasahar kuɗi 10

Vanguard ta wallafa cewa kamfanin ya kuma amince da kamfanonin fasahar kuɗi 10 da za su bai wa masu zuba jari damar neman hannun jarin.

Ga jerin sunayensu:

  1. Bamboo
  2. Flutterwave
  3. InvestNaija
  4. Ladder
  5. Moniepoint
  6. Paga
  7. Payaza
  8. PiggyVest
  9. Vetiva Invest
  10. We.yan

Kamfanonin sadarwa da NGX

Hanyoyin sadarwar wayar hannu da aka amince da su su ne:

  1. Airtel SmartCash
  2. MTN MoMo
Dangote da ma'aikatan shi
Alhaji Aliko Dangote da wasu jami'an shi. Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Za a fara sayen hannun jarin

Masu son sayen hannun jarin a kasuwar hannayen jari ta Najeriya za su buƙaci amfani da kamfanin dillalan hannayen jari da ke da lasisi, ba tare da sayen hannun jarin kai tsaye daga kamfanin ba.

Kara karanta wannan

Ana zargin Bello Turji da kai mummunan hari a Sokoto da aka sace mutane 40

Idan mutum bai da asusun cinikin hannayen jari, zai buƙaci buɗe ɗaya a kamfanin dillalan hannayen jari da Hukumar Kula da Kasuwar Hannayen Jari (SEC) da Kasuwar Hannayen Jari ta Najeriya (NGX) suka amince da shi.

Yawancin kamfanonin dillalan hannayen jari yanzu suna ba da damar yin rajista ta yanar gizo, inda ake buƙatar bayanan BVN, katin shaida da hoton fasfo domin tabbatar da bayanan mai nema.

Kafin a tura kuɗi, ya kamata mai zuba jari ya tabbatar da cewa kamfanin dillalan hannayen jarin yana da lasisi daga SEC ko NGX.

Yadda ake haɗa asusun CSCS

A wani rahoton, mun kawo cewa hannayen jari ba a bayar da su a takardar shaidar mallaka, domin ana adana su ne ta hanyar lantarki a CSCS.

Lokacin da mutum ya buɗe asusun cinikin hannayen jari, kamfanin dillalan hannayen jarin yawanci zai taimaka masa wajen buɗe ko haɗa asusun

Da zarar an fara cinikin hannayen jarin kuma aka ware wa mai zuba jari hannun jari, za a saka su kai tsaye cikin wannan asusun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng