Atiku Ya Fito da Cikakken Tsarin Dawo da Tallafi don Man Fetur Ya Yi Araha

Atiku Ya Fito da Cikakken Tsarin Dawo da Tallafi don Man Fetur Ya Yi Araha

  • Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zo da irin na shi tsarin na karya farashin litar fetur
  • Idan Atiku ya zama Shugaban Najeriya a 2027, zai kawo wa jama’a sauki ba tare da bude damar satar kudin mai ba
  • Wannan sabon tsari yana nufin rage radadin tattalin arziki da aka shiga musamman daga karshen Mayun 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya cigaba da tallata muradinsa na maido tallafin man fetur.

Idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya a 2027, ‘dan takaran na ADC zai dawo da tsarin tallafin da aka yi watsi da shi.

Atiku fetur
Atiku Abubakar a gidansa da hoton wani mai mota yana shan man fetur Hoto: Atiku Abubakar (Facebook) / Getty Images
Source: UGC

Atiku ya fitar da jawabi a kan dabarar AERP

A wani jawabi da hadiminsa, Phrank Shaibu ya fitar a shafin X, Atiku Abubakar ya shaida wa ‘yan Najeriya tsarinsa na AERP.

Kara karanta wannan

Abin da Atiku zai yi don magance rashin tsaro cikin kwana 100 idan ya zama shugaban kasa

AERP dabaru ne da Atiku Abubakar zai bi wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya, don haka ya bar zabi ga jama’a a Junairun 2027.

Gwamnatin Atiku za ta yi kokarin rage farashin man fetur ta hanyar kawo tsari mai kama da na tallafi da Bola Tinubu ya cire.

Atiku: AERP zai maido tallafin man feturWS

Wannan karo ya ce za a samar da tallafi na gaskiya, kayyadajje kuma wanda za a samu masu zaman kansu suna bin lissafin.

Ya ce da wadannan dabaru za a sauko daga farashin fetur kuma dage wajen ganin matatun cikin gida suna tace danyen mai.

"Dabarar da zan kawo ba dawo da tsohon tsarin tallafi ba ne. Za mu rabu da tallafi, mu koma wa shigo da mai zuwa samar da shi a gida.
"A tashi daga harka da dillalai zuwa matatun Najeriya, kuma a daina kintace a cikin duhu, a koma lissafin ganguna."

Kara karanta wannan

Atiku ta tayar wa Tinubu hankali kan kudirin dawo da tallafi idan ya yi nasara

- Phrank Shaibu

Za a cire rashin gaskiya a tallafin mai

Daily Trust ta ce a tsarin AERP, tallafin da za a biya ya ta’allaka da gangunan man da aka hako, adadin da ba a san bi a yanzu.

A gwamnatinsa, za a san nawa ne kudin mai kuma za a san su wane ne ‘yan Najeriya masu cin moriyar ragin kudin man da aka yi.

Hadimin ya ce a sanarwar:

"Za mu yanke rangwamen nawa Najeriya za ta iya yi. Ba za mu sa tallafi ba da farko, sannan sai daga baya a san nawa ne kudin."

Sai an bi kwa-kwaf kafin ba kowace matata danyen man da aka yi wa rangwame kuma kowa zai san a kan farashin da aka saida.

Ba za a yi amfani da sunan jiragen bogi, a yi karyar an shigo da man fetur ko a buga takardu saboda a tatsi kudi da sunan tallafi ba.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Atiku ya fadi lokaci na karshe da zai yi takarar shugabancin Najeriya

Za a duba girma da karfin matata wurin raba danyen da nufin ganin ba a yi son kai ba tare da tanadin ukuba ga masu saba doka.

Atiku za su iya doke Tinubu a 2027?

Tsohon hadimin Bola Tinubu, Hakeem Baba-Ahmed aka ji labari ya nanata cewa APC za ta riga rana faduwa a zaben da za a shirya 2027.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya ce APC na fuskantar kalubale mai karfi gabanin zaben 2027, bai ganin Bola Tinubu zai koma mulki a badi.

Tsohon hadimin Tinubu ya yi nazarin zaben Osun, ya ga 'yan adawa sun doke APC, sai dai bai fadi wani 'dan takaran zai ci zaben ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng