Kamar Atiku, An Samu 'Dan Takarar Shugaban Kasa da zai Dawo da Tallafin Man Fetur
- Dan takarar shugaban kasa a 2027, Omoyele Sowore ya ce ba zai cire tallafin man fetur ba idan aka zaɓe shi shugaban ƙasar Najeriya
- Ya ce za a iya ci gaba da biyan tallafin tare da magance cin hanci da rashawa da kuma ɓarnar da ke tattare da tsarin wanda ke nakasa kasar
- Dan takarar AAC ya ce farfaɗo da matatun man Najeriya zai rage kuɗin shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje wanda zai habaka kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Nigeria – Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Sowore ya ce cire tallafin ya ƙara tsananta halin ƙuncin tattalin arziki da ’yan Najeriya ke fuskanta, yana mai cewa gwamnati na iya ci gaba da tallafin tare da magance cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Shirin Atiku na dawo da tallafin mai na iya tsorata wasu yan ƙasashen waje

Source: Facebook
A hira da ya yi da kafar Arise a ranar Talata 25 ga watan Agusta, 2026, Omoyele Sowore ya ce idan ya ci zabe, zai kawo karshen almundahanar da ke tattare da tsarin tallafin man fetur.
Abin da Sowore ya ce kan tallafin man fetur
A tattaunawar, Sowore ya ce gwamnati za ta iya ci gaba da biyan tallafin tare da magance cin hanci da rashawa da kuma almundahanar da ke tattare da tsarin, maimakon ɗora nauyin gazawar gwamnati kan talakawa.

Source: Getty Images
Ya ce:
“Tsarina game da tallafin shi ne ba za a cire shi ba. Don haka, batun cin hanci da rashawa ne. Mutumin da zai iya tallafa wa talakawa, sannan a lokaci guda ya yaƙi cin hanci da rashawa, shi ne mutumin da ya kamata ku zaɓa, ba wanda ya kasance cikin waɗanda suka wawure kuɗaɗen tallafin a baya ba, wanda ya amfana da cutar da talakawa, sannan yanzu yake cewa ya kamata a ɗora wa talakawa nauyin wannan gazawa."
Sowore ya fadi tsarinsa idan ya ci zabe
Sowore ya ce ya bayyana matsayinsa kan tallafin a cikin manufofin da ya tsara, ciki har da yadda gwamnatinsa za ta samu kuɗin ci gaba da shirin idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasa.
Dangane da yadda zai samar da kuɗin tallafin, Sowore ya ce gwamnatinsa za ta farfaɗo da matatun man fetur guda huɗu na Najeriya tare da ƙara yawan tace man fetur a cikin gida.
Ya ce hakan zai taimaka wajen rage kuɗin da ake kashewa wajen shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje tare da saukaka wa yan kasa.
Sowore zai bada ilimi kyauta
A wani labarin, kun ji cewa mai rajin kare hakkin bil adama, Omoyele Sowore ya fitar da tsarin ilmi na jam'iyyarsa ta AAC yayin da ake shirin zaben 2027.
Sowore ya yi alkawarin cewa ilimi zai zama kyauta daga makarantar firamare har jami'a, kuma ba za a biya kudin jarrabawar kammala sakandare na WAEC ko NECO ba.
Takardar manufofin da ya fitar ta kunshi matakai 20 da suka shafi abubuwan more rayuwa, fasaha, malamai da walwalar dalibai wanda ya ce ya tanadar wa jama'ar kasar nan.
Asali: Legit.ng
