'Yadda Atiku Ya So a Zare wa 'Yan Najeriya Tallafin Fetur a Gwamnatin Obasanjo'

'Yadda Atiku Ya So a Zare wa 'Yan Najeriya Tallafin Fetur a Gwamnatin Obasanjo'

  • Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Accord, Dr. Gbenga Olawepo-Hashim, ya kira Atiku Abubakar “jagoran cire tallafin mai” a Jamhuriya ta hudu
  • Hashim ya ce sauya matsayar Atiku kan cire tallafin mai na baya-bayan nan na bukatar ya yi wa ’yan Najeriya bayani tare da neman afuwa
  • Ya ce Atiku, Bola Tinubu da Peter Obi sun yi yakin neman zabe ne kan cire tallafin mai a zaben shugaban kasa na 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Accord, Dr. Gbenga Olawepo-Hashim, ya bayyana tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin “jagoran cire tallafin mai” a Jamhuriya ta hudu a Najeriya.

Hashim ya ce sauya matsayar da Atiku ya yi a baya-bayan nan kan cire tallafin mai na bukatar tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wa ’yan Najeriya bayani tare da neman afuwa.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku ya rikita Najeriya da maganar maido tallafin man fetur

An soki Atiku kan batun dawo da tallafin fetur
Atiku Abubakar na jawabi a wajen yakin neman zaben gwamnan Osun na ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A cewarsa, sauya matsayar ‘yan siyasar da a baya suka goyi bayan cire tallafin mai ya jawo tambayoyi kan gaskiya da kuma asalin sababbin matsayinsu, cewar rahoton Vanguard.

“Wasu ‘yan takarar da suka yi yakin neman zabe a zaben da ya gabata domin a cire tallafi yanzu sun sauya matsayinsu, ba tare da ma sun nuna nadamar rashin tausayi da suka nuna wa jama’a a baya ba.” In ji shi.

Gbenga Hashim ya soki Atiku Abubakar

Hashim ya soki Atiku musamman kan sauya matsayinsa ba tare da amincewa da cewa ya taba goyon bayan cire tallafin mai ba, jaridar Leadership ta kawo labarin.

"Sauya matsayin Atiku kan cire tallafi ba tare da neman afuwa ba rashin gaskiya ne. Idan ka sauya matsayinka saboda yanayi ko hujjoji sun sauya, ka gaya wa ’yan Najeriya dalilin da ya sa ka sauya."
"Babu laifi mutum ya sauya ra’ayinsa. Abin da bai dace ba shi ne mutum ya yi kamar bai taba rike wannan matsayi ba tun farko.” In ji shi

Kara karanta wannan

Abin da Atiku zai yi don magance rashin tsaro cikin kwana 100 idan ya zama shugaban kasa

Ya ce Atiku, Shugaba Bola Tinubu da Peter Obi duk sun yi yakin neman zabe ne kan cire tallafin mai a zaben shugaban kasa na 2023, yayin da shi, Omoyele Sowore da Yarima Adewole Adebayo suka yi adawa da manufar.

'Atiku ya dade yana goyon bayan cire tallafi'

A cewar Hashim, matsayin Atiku kan cire tallafin mai ya kasance tun kafin gwamnatin Tinubu, inda ya bayyana tsohon mataimakin shugaban kasar a matsayin daya daga cikin manyan mutanen farko da suka goyi bayan cire tallafin mai da kuma mayar da kamfanonin gwamnati gaba daya hannun masu zaman kansu a Jamhuriya ta hudu.

“Gaskiyar magana ita ce, tun kafin Tinubu, a fagen siyasar kasa, Atiku ne jagoran ra’ayin cire tallafin mai da mayar da kamfanonin gwamnati gaba daya hannun masu zaman kansu a wannan jamhuriya, tare da tawagarsa ta tattalin arziki."
“Mun yi musu tirjiya sosai a farkon zamanin gwamnatin Obasanjo.” In ji shi.
Olawepo Hashim ya soki Atiku
Gbenga Olawepo Hashim na jawabi a wajen taron coci Hoto: Gbenga Olawepo Hashim
Source: Facebook

Shugaban APC ya soki Atiku kan dawo da tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya soki Atiku Abubakar, kan alƙawarinsa na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a 2027.

Nentawe Yilwatda ya bayyana matakin na Atiku a matsayin tsananin yunƙurin neman mulki, yana mai cewa hakan na iya jefa tattalin arzikin Najeriya cikin ƙarin matsaloli. Re

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng