Kaico: An Tsinci Gawar Budurwa a Wani Yanayi bayan Ta Yi Faɗa da Saurayinta a Kaduna
- Rundunar ’Yan sanda a Kaduna ta kama wani mutum kan zargin kashe budurwarsa a karamar hukumar Chikun
- ’Yan sanda sun ce wanda ake zargin shi ne mutum na ƙarshe da ya yi magana da marigayiyar kafin a gano gawarta a yankin Romi
- Wanda ake zargin ya amsa cewa sun yi faɗa a ɗakinsa kan kiran waya da ya yi da wata mace ta daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama wani mutum kan zargin kashe budurwarsa.
Rundunar ta ce wanda ake zargin shi ne mutum na ƙarshe da ya yi hulɗa da marigayiyar kafin a gano gawarta a yankin Romi, ƙaramar hukumar Chikun ta jihar.

Source: Twitter
An tsinci gawar budurwa a Kaduna
Tashar Channels tv ta ce kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa lamarin ya faru ne ranar 5 ga Satumba, 2026.
Hakan ya biyo bayan ’yan sanda sun samu rahoton gano gawar wata Rebecca Jeremiah a gefen titin Mai Angwa da ke Romi.
Jami’an binciken manyan laifuka daga ofishin ’yan sanda na Romi sun je wurin da lamarin ya faru, inda suka garzaya da matar zuwa Asibitin St. Gerald da ke Kakuri, inda wani likita ya tabbatar da rasuwarta.
An ajiye gawarta a ɗakin ajiye gawarwaki na asibitin domin gudanar da gwajin gawar kafin mika ta ga yan uwanta.
Yadda aka kama wanda ake zargi
A cewar sanarwar ’yan sandan, Jatau shi ne mutum na ƙarshe da ya kira marigayiyar domin ta haɗu da shi a wani wurin shan giya da ke Romi.
Daga baya jami’an tsaro sun gano inda yake tare da kama shi a wurin aikinsa, wato kamfanin Tomato Jos da ke yankin Maraban Jos, ƙaramar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
A lokacin da ake yi masa tambayoyi, ’yan sanda sun ce wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi faɗa da marigayiyar a ɗakinsa ne kan wani kiran waya da wata mace ta yi.
A cewar wanda ake zargin, rikicin ya yi sanadin mutuwar matar, bayan haka ya jefar da gawarta a wani fili kusa da gidansa da nufin ɓoye laifin.
’Yan sanda sun ce wanda ake zargin yana hannunsu yayin da ake ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala binciken, cewar Daily Post.

Source: Original
Kwamishina yan sanda ya yi gargadi
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Rabiu Muhammad, ya yi Allah-wadai da duk wani nau’in tashin hankali, inda ya buƙaci jama’a su riƙa warware saɓani cikin lumana.
Rundunar ta kuma sake tabbatar da aniyarta ta tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa da kuma gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifuka a gaban kotu.
Matashi ya kashe budurwa a otal
Kun ji cewa wani matashi Ali Haruna, ya amsa zargin kashe wata budurwa mai suna Aisha tare da fille mata kai a wani otal da ke ƙaramar hukumar Girei ta Jihar Adamawa.
Jami'an tsaro sun kama Haruna, wanda ɗan asalin Kaleri ne da ke Maiduguri a Jihar Borno, bisa zargin kisan matar a wani otal da ke Girei, kusa da Yola.
Asali: Legit.ng

