Sabon Farashin Man Fetur
Kungiyar dlillalan fetur ta fara nazarin farashin NNPCL. Kamfanin mai na kasa ya sanar da farashin fetur da za a sayar ga yan kasuwa daga matatar Fatakwal.
Jama'a sun fara bayyana mamakinsu bayan matata Dangote ta tallata man fetur da ta ke cewa, wanda ta ce ya na da inganci da sauki kuma mai kyau ga muhalli.
Hukumar kwastam za ta sayar da man fetur da araha a jihar Adamawa. Hakan na zuwa ne bayan kama man fetur ana shirin fita da shi daga Najeriya ta barauniyar hanya.
Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya bayyana cewa fetur din da za a rika samarwa daga matatar Port Harcourt da ke Rivers, na gidajen man kamfanin ne kawai.
A wannan rahoton za ku ji cewa kungiyar Petroleum Products Retail Outlet Owners Association of Nigeria ta fadi matsayarta a kan labarin kara mata farashin fetur.
Kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta bi jerin wasu daga cikin yan kasar nan wajen yin murna da gyara matatar mai ta Fatakwal, tare da fadin yadda za ta taimaka.
Kungiyar PETROAN ta ce farashin man fetur a matatar Fatakwal ya kai N1,045 wanda ya fi na Dangote tsada da. N75. Ana sa ran NNPCL zai daidaita farashin
'Yan kasuwar mai sun nuna farin cikin dawowar matatar Fatakwal inda suka ce akwai yiwuwar farashin fetur ya sauka saboda gasa da kuma wadatar man a kasuwa.
Gwamnati ta ce ana sa ran manyan motocin dakon mai guda 200 za su dinga loda fetur kullum daga matatar mai ta Fatakwal mai karfin tace ganga 600,000 kullum.
Sabon Farashin Man Fetur
Samu kari