
Wahalar man fetur a Najeriya







Hukumar NEITI ta ce daga shekarar 2017 zuwa 2021, barayi sun sace ganguna fiye da miliyan 200 na arzikin danyen mai, an jawowa Najeriya asarar Naira Tiriyan 4.3

Wata kungiya mai suna Nigeria Accountability Monitors (NAM), ta soki Kungiyar Ma'aikatar Shari'a na Najeriya kan cewa sun bukaci a sauke shugaban kamfanin NNPCL.

A watan Disamban 2023, kamfanin zai warewa matatar litan danyen mai miliyan 6, da zarar an rattaba hannu a yarjejeniyar, fetur zai samu a Najeriya cikin sauki.

Bola Tinubu ya fadi inda Najeriya za ta koma samun kudin shiga a maimakon fetur, za a yaki masu hako ma’adanai a boye, sannan za a kawo tsare-tsaren saukaka harkar.

Danyen man da ake bukata domin a samar da man fetur, man jirgi da dizil ya zama aiki, a gama gina wasu kananan matatu domin a rika tace danyen mai a Najeriya.

Wata tanka makare da man fetur ta yu bindiga yayin da take kokarin sauke mai da tsakar rana a Hayin Rigasa, ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Sanatoci sun fara binciken yadda Gwamnati ta kashe Naira Tiriliyan 11 a shekaru 13. An yi ta kashe kudi daga zamanin marigayi Ummaru ‘Yar’adua zuwa yau.

Al'umma su na faman kokawa a game da 'dan karen tsadar rayuwa. Man fetur ya na cigaba da kara tsada a Najeriya duk da kamfanin NNPCL ya musanya zargin rashin kaya.

Gobara a wani gidan mai da ke jihar Ogun ta lakume rayukan mutane biyu tare da raunata wasu mutane da dama yayin da ake juyen bakin mai a cikin tanka.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari