Ana Wata ga Wata: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Shirya Dawo da Litar Fetur N200 a Najeriya
- Gbenga Olawepo-Hashim ya ce babu dan Najeriya da zai sayi litar fetur sama da N610 a karkashin gwamnatin Accord
- Dan takarar shugaban kasa na Accord ya ce farashin fetur zai iya sauka zuwa N200 idan an daidaita kudin samarwa da canjin Naira
- Ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan tsarin kudin man fetur tare da bayyana dukkan kudade da ribar da ake samu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Accord, Gbenga Olawepo-Hashim, ya ce bai kamata ’yan Najeriya su rika biyan fiye da N610 kan kowace litar fetur ba.
Ya yi alkawarin cewa idan Accord ta karbi mulki farashin fetur zai dawo N605, yana mai cewa farashin zai iya sauka zuwa N200 idan an daidaita kudin samar da fetur da darajar musayar Naira.

Source: Facebook
Taya za a iya dawo da fetur N200?
A rahoton Channels tv, Hashim ya ce N605 zai zama farashin farko a gwamnatinsa, yana mai cewa babu maganar dawo da wani sabon tsarin tallafin mai tsarinsa.
Ya kuma jaddada cewa rage farashin ba zai kasance ta hanyar rage kudaden shiga na gwamnati ko na Asusun Tarayya (FAAC) ba.
“N605 kan kowace lita shi ne farashin farko mai dorewa na fetur a gwamnatina, babu wanda zai sayi fetur sama da N610 a karkashin gwamnatinmu. Zai iya sauka har N200,” in ji shi.
Shin Hashim zai dawo da tallafin mai?
Hashim ya ce abin da zai sa a samu wannan sauki ba wai sake dawo tallafin mai ba ne, sai dai gyara matsalar da ya bayyana a matsayin karkatacciyar hanyar lissafin kudin man fetur.
Dan takarar ya dade yana adawa da cire tallafin man fetur, inda ya bayyana dalilan da aka bayar a baya na cire tallafin a matsayin “sihirin lissafi”.

Kara karanta wannan
An gano manyan hadurra 3 a shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ga 'yan Najeriya
Ya ce ya kamata Najeriya ta fara gano ainihin kudin da ake kashewa wajen hakowa, tacewa, safarar man fetur da kuma rarraba shi kafin a ce gwamnati na biyan tallafi ga masu amfani da shi.
Ya bukaci binciken kudin man Najeriya
Hashim ya ce Najeriya ta saba amfani da farashin kasuwar duniya wajen tantance kudin danyen mai ko tataccen mai a cikin gida, maimakon gano ainihin kudin da ake kashewa wajen samar da man da kai shi ga masu amfani da shi a Najeriya.
Dan takarar Accord ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan tsarin kudin man fetur a Najeriya.

Source: Getty Images
Ya ce binciken ya kamata ya shafi hakar danyen mai, kwangiloli, saye da samar da kayayyaki, tace man fetur, sufuri, ajiya, inshora, ayyukan bututun mai da rarrabawa.
Ya ce hakan zai taimaka wajen gano ainihin kudin samar da kowace litar fetur da kai ta kasuwar Najeriya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Peter Obi ya juyawa Atiku baya
A wani labarin, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi ya bayyanaNmatsayarsa kan batun dawo fa tallafin man fetur a Najeriya.
Peter Obi ya ce ba ya tare da matssyar Atiku Abubakar, inda ya sake jaddada goyon bayansa ga cire tallafin man fetur a Najeriya.
Asali: Legit.ng
