Fadar Shugaban Kasa Ta Sake Gano Lam'a a Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Fetur

Fadar Shugaban Kasa Ta Sake Gano Lam'a a Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Fetur

  • Fadar Shugaban Kasa ta ce Atiku ya sauya matsayarsa sau da dama cikin mako guda kan shirin dawo da tallafin man fetur
  • Bayo Onanuga ya bukaci Atiku ya bayyana abin da yake nufi da “targeted subsidy” da yadda za a dauki nauyin shirin
  • Fadar ta ce matsalar tsadar rayuwa ba ta takaita ga farashin fetur ba, tana bukatar magance matsalolin noma, tsaro, canjin kudin waje da sufuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Fadar Shugaban Kasa ta zargi Atiku Abubakar, da yin siyasa da shirin dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaben 2027.

Fadar ta kuma bayyana cewa Atiku yana cikin rudani kan manufar da yake son aiwatarwa, tana mai cewa kalaman da ya yi na baya-bayan nan sun haifar da tambayar ko da gaske yana gabatar da wata manufa ta tattalin arziki ne ko kuma yana kokarin cin moriyar radadin da ‘yan Najeriya ke ciki na dan lokaci.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Atiku na neman bahasi daga Tinubu kan kudaden cire tallafi

Fadar shugaban kasa ta taso Atiku a gaba
Atiku ya ce zai dawo da tallafin fetur Hoto: @atiku
Source: Twitter

Bayo Onanuga, mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yada labarai da dabarun sadarwa, ya bayyana hakan a wata sanarwa a shafinsa na X ranar Laraba, 26 ga watan Agustan 2026.

‘An ji bayani uku daban-daban'

Onanuga ya ce cikin mako guda, ‘yan Najeriya sun ji bayanai guda uku daban-daban daga bangaren Atiku game da abin da gwamnatinsa za ta yi kan tallafin man fetur.

Ya ce da farko, Paul Ibe, mai magana da yawun Atiku, ya bayyana cewa Atiku zai dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi, sannan daga baya a cire shi a hankali.

A cewar Onanuga, Ibe ya bayyana tallafin a matsayin matakin wucin gadi da zai bai wa ‘yan Najeriya da ‘yan kasuwa damar farfadowa daga matsin tattalin arziki.

Sai dai daga baya wani babban hadimin Atiku, Phrank Shaibu, ya ce bayanin Ibe bai samu izini ba kuma ya karkatar da ainihin matsayin dan takarar.

Kara karanta wannan

An gano manyan hadurra 3 a shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ga 'yan Najeriya

Hadiman Atiku sun ba da bayanai mabambanta

Onanuga ya ce Shaibu ya bayyana cewa Atiku ba zai sanya wata takamaiman ranar da za a kawo karshen tallafin ba.

A cewarsa, tallafin zai ci gaba ne har sai an kara habaka tace danyen mai a cikin gida, samar da man fetur ya daidaita, gasa ta karu, sannan kasuwa ta iya samar da farashi mai sauki ba tare da dogaro da tallafin gwamnati ba.

Sai dai bayan sa’o’i kadan, Atiku da kansa ya shiga batun, inda ya ce matsayinsa bai sauya ba.

Atiku ya sake jaddada cewa zai dawo da abin da ya kira “tallafi na musamman”, yana mai cewa zai mayar da ikon sayen kayayyaki ga ‘yan Najeriya.

Fadar shugaban kasa ta ce akwai rudani

Onanuga ya ce wannan ba batun amfani da kalmomi daban-daban ba ne kawai, illa dai babban sabani ne wajen tsara manufofin tattalin arziki.

Ya tambayi dalilin da ya sa wani babban hadimin Atiku ya ce tallafin zai kasance na wucin gadi kuma daga baya a cire shi, yayin da wani ya musanta hakan ya gabatar da wani tsari dabam.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya saba da Atiku, ya bayyana babbar matsalar dawo da tallafin fetur

Hakazalik ya kuma tambayi dalilin da ya sa Atiku ya shiga tsakani daga baya ya sake tabbatar da matsayinsa na farko.

Onanuga ya ce ‘yan Najeriya sun cancanci samun cikakken bayani, ba kuma a gwada manufofin tattalin arziki ana canza su lokaci zuwa lokaci ba.

‘Tsadar rayuwa ba farashin mai kawai ba ne’

Fadar Shugaban Kasa ta ce matsalar tsadar rayuwa a Najeriya ba ta samo asali ne daga farashin man fetur kadai ba.

Onanuga ya lissafa abubuwan da suka hada da yawan amfanin gona, rashin tsaro, canjin darajar kudin waje, sufuri, ajiyar kayayyaki, ambaliyar ruwa, tsadar kayan noma, yawan kudin da ke yawo da kuma matsalolin samar da kayayyaki.

Ya ce shirin tattalin arziki mai inganci dole ne ya magance wadannan matsaloli gaba daya, maimakon mayar da matsalar tsadar rayuwa gaba daya kan farashin man fetur.

Fadar shugaban kasa ta dura kan Atiku
Shugaban kasat Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Atiku ya kalubalanci gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya kalubalanci gwamnatin tarayya kan kudaden cire tallafi.

Atiku ya bukaci gwamnatin da ta yi wa ’yan Najeriya bayani kan yadda aka kashe kudaden da aka samu bayan cire tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng