Sarkin Musulmi Ya Yi Magana kan Kashe Malamar Islamiyya a Kaduna

Sarkin Musulmi Ya Yi Magana kan Kashe Malamar Islamiyya a Kaduna

  • Kungiyar JNI ta yi Allah wadai da kashe malamar Islamiyya, Ummulkhair da taron jama'a suka yi a Mararaban Jos da ke Jihar Kaduna
  • Bugu da kari, JNI ta buƙaci a gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci tare da gurfanar da duk masu hannu a kashe malamar a gaban kotu
  • Ta kuma nemi a binciki zargin da ake yi wa DPO na Mararaban Jos kan mika malamar ga mutanen da suka kashe ta tare da ba iyalan ta diyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI) ta yi Allah wadai da kisan gillan da aka yi wa malamar Islamiyya, Ummulkhair a Mararaban Jos da ke Jihar Kaduna, tana mai bayyana lamarin a matsayin babban laifi.

Kara karanta wannan

Tuban muzuru: Malami ya gargadi gwamnati game da karban tuban yan bindiga

Ƙungiyar, ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar, ta bayyana alhini da kaɗuwa kan lamarin, tana mai cewa hakan na nuna durƙushewar kyawawan ɗabi'u, yaɗuwar bayanan ƙarya da kuma ƙaruwar al'adar ɗaukar doka a hannu.

Sarkin Musulmi da Malamar Islamiyya
Malamar Islamiyya, Ummulkhairi a hagu, mai alfarma Sarkin Musulmi a dama. Hoto: Hassan Muhammad|JNI
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da sakataren JNI, Farfesa Khalid Aliyu, ya fitar a Facebook, ƙungiyar ta ce kisan na daga cikin munanan misalan rashin bin doka da lalacewar ɗabi'u da ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

Gargadi kan yada bayanan karya

Sanarwar ta ce yaɗa bayanan ƙarya, zarge-zargen da ba su da tushe da kuma maganganun tunzura jama'a sun zama makamai masu haɗari da za su iya jefa marasa laifi cikin wulakanci, tashin hankali da mutuwa.

“Babu wata al'umma da za ta dore idan son zuciya ya maye gurbin hujja, kuma taron jama'a ya maye gurbin hukumomin shari'a. Abin takaici, al'ummarmu na ci gaba da kaucewa tafarkin wayewa zuwa dabbanci, inda fushi ya maye gurbin hankali, kuma tashin hankali ya zama ruwan dare,”

In ji sanarwar.

Sarkin Musulmi ya yi ta'aziyya

JNI ta miƙa ta'aziyyarta ga iyalan marigayiyar, da gwamnatin jihar Kaduna, da al'ummar Musulmi da kuma dukkan 'yan Najeriya da wannan al'amari ya shafa.

Kara karanta wannan

Ardo Risku: Mutane 10 da ake zargi da kisan shugaban Miyetti Allah sun shiga hannu

Ƙungiyar ta yi addu'ar Allah Ya jikan Malama Ummulkhairi da rahama tare da ba iyalanta haƙurin jure wannan babban rashi.

JNI Ta kuma yi gargaɗi game da ƙara yaɗuwar al'adar kisan gilla da taron jama'a ke yi, yanke hukunci cikin gaggawa da kuma hukunta mutane ba tare da bin doka ba.

Ta jaddada cewa addinin Musulunci yana ba rayuwar ɗan Adam muhimmanci ƙwarai, kuma ya haramta kashe marasa laifi ba tare da bin tsarin shari'a ba.

Mijin Malamar Islamiyya
Lokacin da aka ba mijin malamar Islamiyya tallafi a Kaduna. Hoto: Abdulkarim Hamisu Assuyudy
Source: Facebook

Buƙatar a binciki DPO a Kaduna

JNI ta yi kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa, gaskiya da adalci kan yadda lamarin ya faru, tare da buƙatar hukumomin tsaro su gano tare da gurfanar da duk waɗanda suke da hannu kai tsaye ko a kaikaice a kisan.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci a binciki zargin da ake yi cewa DPO na Mararaban Jos ya gaza kare marigayiyar, har ma ya miƙa ta ga taron jama'a.

The Sun ta rahoto cewa JNI ta ce idan bincike ya tabbatar da sakaci, rashin ɗa'a ko haɗa baki daga kowane jami'in tsaro, ya kamata a hukunta shi bisa tanadin doka.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya kawo hanyar magance rikicin manoma da makiyaya

Ƙungiyar ta kuma yi kira da a biya iyalan marigayiyar diyya, tare da roƙon gwamnatin Jihar Kaduna da ta ba iyalan tallafin jin ƙai da kuma tallafi na dogon lokaci ga waɗanda marigayiyar ta bari.

Malaman Islamiyya sun bada tallafi

A wani labarin, mun rahoto muku cewa wasu malaman Islamiyya a sassan Najeriya sun ba iyalan Malama Ummulkhairi gudunmawa.

Wanda ya jagoranci tawagar tattara kudin, Abdulkarim Assuyudy ya bayyana cewa sun ba da tallafin ne domin kula da 'ya'yan marigayiyar.

A cikin 'yan kwanaki bayan kashe Malama Ummulkhairi, malaman Islamiyya sun hada sama da N250,000 sun mika ga mijinta a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng